Alkaluman da hukumar kula da kadarorin kasa ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar jiya Talata sun nuna cewa, a cikin rubu’i uku na farkon bana, wato watanni tara da suka gabata, tattalin arzikin manyan kamfanoni mallakar gwamnatin kasar na gudana yadda ya kamata, adadin ribar da suka samu ta karu.
Gaba daya adadin kudin shigar da suka samu, ya kai kudin Sin yuan triliyan 29, adadin da ya karu da kaso 10.9 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.
Alkaluman sun nuna cewa, kamfanoni mallakar gwamnati sun samu ci gaba mai inganci, inda a rubu’i uku na farkon bana, gaba daya adadin kudin da kamfanonin suka kashe a bangaren aikin nazarin kimiyya da fasaha ya karu da kaso 17.5 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, kana ribar da suka samu ta kai kaso 7.2 bisa dari, adadin da ya kai matsayin koli a tarihi.
Hakazalika, adadin harajin da kamfanonin suka biya a wannan wa’adi, ya kai kudin Sin yuan triliyan 2.1, karuwar kaso 15.2 bisa makamancin lokacin bara. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp