Majalisar wakilai ta yi karatu na biyu a kan kudirin da ke neman cire alhakin rajista da kuma daidaita lamuran jam’iyyun siyasa daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) tare da mika shi ga wata hukuma mai zaman kanta.
Kudirin wanda dan majalisa Babajimi Benson da Marcus Onobun ne suka gabatar da shi a zauren majalisa, ta ba da shawarar kafa ofishin rajistar jam’iyyun siyasa, wanda zai kula da rajista, tsari da gudanar da jam’iyyun siyasa a Nijeriya.
- Majalisa Ta Umarci NCC Ta Rufe Dukkanin Shafukan Intanet Na Batsa A Nijeriya
- Hajjin Bana: NAHCON Za Ta Fara Jigilar Maniyyata A Ranar 6 Ga Mayu
Kudirin mai taken “Kudirin dokar da za ta kafa dokar jam’iyyun siyasa, wajen yin rajista da sauran al’amurar jam’iyyun siyasa ta shekarar 2024,”Kudirin dokar da aka gabatar na da nufin gyara tsarin zabe ta hanyar rage wa INEC ayyukan sa ido kan jam’iyyun siyasa.
Da yake jagorantar muhawarar, dan majalisar wakilai, Onobun ya bayyana cewa, kiraye-kirayen sake tsarin zaben Nijeriya na ci gaba da mamaye zukatan jama’a, musamman game da rajista da tsarin jam’iyyun siyasa. Ya bayyana cewa da yawa daga cikin ‘yan Nijeriya sun yi imanin cewa ingancin zabe ya dogara ne kan tsarin ‘yanci, gaskiya, da rashin son kai na rajistar jam’iyyun siyasa da gudanar da zabe. Sai dai ya ce, ana ci gaba da nuna damuwa a kan kura-kuran da ake tafkawa a zaben da ke da alaka da INEC, ko daidai ko kuskure.
Ya kara da cewa, da yawan al’ummar Nijeriya na ikirarin cewa INEC na wuce gona da iri wajen wasu batutuwa da suka hada da rajista da tsara jam’iyyun siyasa, sa ido kan hadewar jam’iyya da hadakar jam’iyyun, da gudanar da zabukan shugaban kasa, ‘yan majalisar tarayya, gwamnoni, da na ‘yan majalisun jihohi. A cewarsa, wadannan ayyuka na sa hukumar zabe ta yi wahalar mai da hankali sosai kan aikinta.
Kudirin ya kuma nemi kafa wata hanyar warware takaddama don magance rikice-rikicen da suka shafi jam’iyyun siyasa, mambobinsu, ‘yan takara masu zaman kansu, da kuma kawance. Bugu da kari, ta tanadi hukunci kan keta haddi da bayar da shawarar gyara ga dokar zabe ta 2022 don cire rajistar jam’iyyun siyasa daga hukumar INEC.
Bayan gabatar da shawarwari, an mika kudirin ga kwamitin majalisa mai kula da harkokin zabe da kwamitin jam’iyyun siyasa domin ci gaba da tattaunawa a kansa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp