A wajen wani muhimmin taron jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin da aka kammala kwanan baya, an zartas da wani kuduri mai nasaba da ci gaba da zurfafa yin gyare-gyare a gida daga dukkan fannoni, da kara zamanantar da kasar Sin.
Kudurin mai kalmomi dubu 22, dake kunshe da matakan yin gyare-gyare na zahiri guda 300, ya shafi fannoni daban-daban na mulkin kasa, ya kuma tsara taswirar ci gaba da zurfafa yin kwaskwarima a gida daga dukkan fannoni, da daukaka ci gaban zamanantarwa irin ta kasar Sin.
- Mataimakin Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kare Jama’a Daga Fadawa Hadurra Yayin Aikin Shawo Kan Ambaliya
- Majalisar Wakilai Ta Ki Amincewa Da Bukatar Tinubu Na Sake Karbo Bashi
Ana iya ganin cewa a cikin kudurin, akwai manyan tsare-tsare daga fannoni da dama, akwai kuma matakan zahiri da za’a dauka. Kaza lika, abu mai muhimmanci a nan shi ne, ba batun yin gyare-gyare a harkokin mulkin kasa kawai kudurin ya mayar da hankali a kai ba, har ma da tsara manyan tsare-tsaren da suka shafi kara bude kofar kasar ga kasashen ketare, ciki har da fadada bude kofa a fannin tsari, da zurfafa yin kwaskwarima ga tsarin cinikin waje, da zurfafa yin gyare-gyare ga tsarin zuba jari na baki ’yan kasuwan waje, da na daidaita harkokin zuba jari ga kasashen waje, da kyautata tsarin bude kofa a yankuna daban-daban, da ci gaba da inganta aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” tare, al’amuran da suka samar da babban zarafi ga zuba jarin waje, gami da na sassan kasa da kasa.
Akwai yakinin cewa, manufar kasar Sin ta fannin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a sabon zamanin da muke ciki, za ta kaddamar da sabon mataki na raya al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce: “Idan duniya ta zama mai kyau, kasar Sin za ta yi kyau. Idan kasar Sin ta zama mai kyau, duniya za ta kara yin kyau.” (Murtala Zhang)