Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ziyarci gidan yarin Kuje da ke birnin tarayya Abuja, da ‘yan bindiga suka kai wa farmaki a daren ranar Talata.
Buhari ya kai ziyarar gani da ido a ranar Laraba don ganin irin barnar da ‘yan bindiga suka yi a gidan yarin.
- Sakataren Jin Dadin Alhazai Na Neja Ya Hana Shugaban Hukumar Na Kasa Hawa Jirgi Tafiya Saudiyya
- Shugaban Jam’iyyar APC Na Yankin Ibadan Da Oyo Ya Sauya Sheka Zuwa PDP
LEADERSHIP ta rawaito yadda wasu mahara suka kai hari, inda suka sanadin tserewar fursunoni sama da 800.
Sai dai hukumar da ke kula da gidajen yari, ta ce manya fursunoni da ke tsare kamar su Abba Kyari ba su tsere ba.
Har wa yau, a ranar Talata ne wasu mahara suka farmaki ayarin tawagar shugaban kasa Muhammadu Buhari a Jihar Katsina, lokacin da ake shirin bikin babbar sallah.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa shugaba Buhari zai bar Abuja da yammacin yau Laraba, 6 ga watan Yuli, domin halartar taron kungiyar ci gaban kasa da kasa (IDA) na Afrika a birnin Dakar na kasar Senegal.
Shugaban kasar zai samu rakiyar ministocin harkokin kasashen waje, Geoffery Onyeama; Kudi, Kasafi da Tsare-tsare na Kasa, Zainab Ahmed; da kuma Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Adeniyi Adebayo.
Sauran da ke cikin tawagar sun hada da: gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele; Darakta-Janar, na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar; Darakta-Janar, Ofishin Kula da Bashi, Patience Oniha; da kuma Manajan Daraktan Bankin Masana’antu, Olukayode Pitan.
Ana sa ran shugaba Buhari zai dawo Nijeriya bayan kammala taron na ranar Alhamis 7 ga watan Yuli.