Idan Iyaye sun samu damar hana su shiga yin halayen da basu kamata ba,a gida ta hanyar koya masu tarbiyyar data dace su yi ta abubuwan da basu dace su yi ba.
To kamar dai yadda Hausawa suka ce ba a nan take ba daaka danne Budari ta ka,saboda kuwa ai ba kowanne lokaci bane Iyayen za su kasance tare da su.
- Zaben 2023: Majalisar Dinkin Duniya Da ECOWAS Sun Yi Sabon Gargadi
- Shagalin Murnar Bikin Bazara Ya Gabatar Da Shirye-shirye Masu Ban Sha’awa Ga Sinawa A Duk Duniya
Kamar yadda Iyaye suke sa ido lokaci- lokaci dangane da tarabiyyar ‘ya’yansu tun daga gida, abu mafi dacewa ne su rika ziyartarsu domin gane irin halin da suke ciki dangane tarbiyyar da suka ginasu da ita tun farko tun suna kanana.
Manufar ziyartarsu zuwa wuraren da suke makaranta lokaci zuwa lokaci yin hakan zai sa su gane wanne irin halin ‘ya’yan nasu suke ciki, su kuma su san cewa kowanne lokaci fa ana iya kawo masu ziyarar ba zata.
Idan sun yi amfani da wannan irin dabarar suma ‘ya’yan koda ace sun fara koyon wasu dabi’u wadanda ba za su haifar da da mai ido ba, ga kansu ‘ya’yan, Iyayen, da kuma al’umma balki daya.
Ziyarar na iya sa su canza halin shiga yin koyi dadabi’un da basu kamata ba.
Wasu ‘ya’yan musamman yadda suke mu’amala da abokan da ba nagari ba da suke kodai shekarun su daidai,ko kuma sun fisu da kadan.
Abin ganewa anan shi ne kamar dai yadda na riga na yi bayani tun farko makon daya gabata wato maudu’i na farko.