Kumbon dakon kaya na Tianzhou-3, mai dakon kayayyaki zuwa tashar sararin samaniya ta kasar, ya rabu da babban bangaren tashar na Tianhe a yau Lahadi, da misalin karfe 10:59 na safiya, agogon Beijing, bayan ya kammala dukkan ayyukan da aka tsara zai gudanar.
A ranar 20 ga watan Satumban 2021 ne, kasar Sin ta yi nasarar harba kumbon Tianzhou-3 daga cibiyar harba kumbuna ta Wenchang dake lardin Hainan na kudancin kasar Sin, dauke da kayayyakin da nauyinsu ya kai kimanin ton 6, zuwa tashar ta sararin samaniya.
A yanzu haka, kumbon Tianzhou-3 na cikin yanayi mai kyau kuma a nan gaba, za a sake sarrafa shi ya shiga sararin samaniya.
Talla