Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce kundin tsarin mulkin ƙasar ba ya goyon bayan wani nau’i na zalunci ko wariyar addini.
Tuggar ya faɗi haka ne a birnin Berlin na ƙasar Jamus bayan Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin soja a kan Nijeriya bisa zargin kisan Kiristoci.
- Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma
- Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar
“Ba zai yiwu gwamnati a kowane mataki ta goyi bayan zalunci ba,” in ji Tuggar.
Ya bayyana cewa Nijeriya ƙasa ce da ke cike da bambance-bambancen addinai, kuma matsalar tsaro na shafar Musulmi da Kiristoci baki ɗaya, don haka zargin cewa ana zaluntar Kiristoci kaɗai ba gaskiya ba ne.
Tuggar ya kuma gargaɗi masu ƙoƙarin raba Nijeriya ta fuskar addini, cewa hakan na iya haifar da rikici irin na Sudan.
Ya jaddada cewa Nijeriya tana da cikakken ’yancin addini da bin doka, tare da kiran maganganun Trump a matsayin marasa tushe.













