Kungiyar Arewa New Agenda, mai fafutukar kare martaba da shigar Arewa cikin harkokin kasa, ta yaba wa Shugaban Kasa Ahmed Bola Tinubu bisa tsarin shugabancinsa tun hawansa mulki makonni biyu da suka gabata.
Shugaban kungiyar Sanata Ahmed Abubakar MoAllahyidi ne ya yi wannan yabon a wata ganawa da manema labarai a Abuja ranar Juma’a.
Arewa New Agenda ta bayyana wasu muhimman shawarwari da matakan da shugaban kasan ya dauka tun bayan hawansa mulki, wadanda suka hada da: soke tallafin man fetur, hana yajin aikin da kungiyoyin kwadago suka shirya yi a fadin kasa, da kafa tsarin kudin musaya na Naira bai-daya, da ganawa da shuwagabannin hukumomi masu muhimmanci tare da kai ziyara a cibiyoyin tsaro da tattara bayanan sirri da sauransu.
A cewar MoAllahyidi, “Wadannan matakai sun nuna jajircewar Shugaba Tinubu wajen tunkarar muhimman al’amurra a kasar nan da kuma samar da jagoranci nagari a harkokin mulki”.
“Nade-naden da Shugaba Tinubu ya yi ya haifar da samun kwarin gwiwa a kan ingantuwar tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa”.
“Muna farin ciki da cewa shugaban kasa Tinubu, wanda kungiyar ta goyi bayansa a lokacin da yake neman takararsa a jam’iyyar APC kuma ya lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2023, ya fara aikinsa da kafar dama.”
“Shugaba Tinubu ya yanke shawarar nada masu ba da shawara na musamman guda takwas, kuma wannan matakin ya samu karbuwa da farin ciki a fadin kasar nan, ciki har da ‘yan adawa. Wani abin lura a cikin wannan ci gaban shi ne babu wata adawa ko rashin jituwa dangane da wadannan nade-nade, wanda ke nuni da goyon bayan zaben da aka yi wa shugaban kasar.
“Wani nadin da ya sanya farin ciki a fadin kasar nan shi ne na mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro. ‘Yan Nijeriya na da kyakkyawan fata na cewa Shugaba Tinubu zai magance kalubalen tsaro yadda ya kamata a wannan karon”.
A baya dai ANA ta jaddada cewa nasara ko gazawar da Tinubu zai samu zai ta’allaka ne a kan ayyukansa na yaki da rashin tsaro da cin hanci da rashawa, wadanda su ne manyan batutuwa biyu da suka addabi al’ummar kasar nan.
Daga cikin fitattun wadanda aka nada akwai Malam Nuhu Ribadu, wanda a baya ya rike mukamin Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) a shekarar 2003. Idan aka duba, Ribadu, tarihinsa na nuna irin kishinsa, sadaukarwa, da kwazonsa na musamman wajen yaki da cin hanci da rashawa. A lokacin da yake rike da mukamin a hukumar ta EFCC, ya sa ido a kan kafa cibiyar horarwa a kan nazarin manyan laifuka da bincike, wanda hakan ya kara tabbatar da martabar hukumar a matsayin babbar hukumar tabbatar da doka a Afirka.
Ribadu ya jajirce wajen neman adalci har aka karrama shi a matsayin wanda ake girmamawa a matsayin dan gwagwarmayar yaki da cin hanci da rashawa a duniya. Kin karbar cin hancin Naira miliyan 30 a shekarar 2005 da kuma cin hancin dala miliyan 15 daga hannun tsohon gwamna a 2007 a shekarar 2007 ya zama abin kwatance game da da’ar aiki.
Bugu da kari, Ribadu ya taka muhimmiyar rawa wajen fitar da Nijeriya daga cikin jerin kasashen kungiyar FATF, da samun damar shigarta kungiyar Egmont, da kuma tabbatar da janye Jami’an da ke sanya ido a kan manyan laifukan kudi a Baitul-malin Amurka daga Nijeriya.
A karshen taron dai, Arewa New Agenda ta yaba wa shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu bisa kyakkawan jagorancinsa da tsarin gudanar da mulkinsa a cikin makonni biyun farko da hawansa karagai. Kungiyar ta yi imanin cewa, matakin da shugaban kasar ya dauka da abubuwan da yake aiwatarwa ne ya sanya Nijeriya ta fara jin kamshin kyakkyawar makoma.