Kungiyar Kwato Hakkin Fulani (FGDRI), ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi adalci kan kashe-kashen da ake yi wa makiyaya a jihohin Kaduna da Taraba, inda ta ce kisan kare dangi ne.
Salim Musa Umar, shugaban kungiyar, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnati ta shiga tsakani domin ceto su daga mugun halin da suke ciki don tabbatar da zaman lafiya.
- Mutum 30 Sun Nutse A Ruwa Yayin Tsere Wa Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara
- An Cafke Wani Mutum Da Ya Yi Wa ‘Yar Uwarsa Mara Hankali Fyade A Kebbi
A cewar shugaban, “A ‘yan kwanakin nan, kafafen yada labarai sun cika da hotunan wasu makiyaya na Fulbe da aka yi wa yankan rago a jihohin Taraba da Kaduna.
“Kungiyar ta Fulbe ta damu matuka da wadannan baragurbi, musamman na baya-bayan nan da suka faru a Bali da ke Taraba da Birnin Gwari a jihar Kaduna.”
Kungiyar ta lura cewa a karamar hukumar Bali, wasu gungun ‘yan banga dauke da makamai sun farmaki wasu makiyayan da ba a san ko su wanene ba, inda suka yi zargin cewa an kai musu hari ba tare da kariya ba tare da yi musu kisan kiyashi da musu aikata laifukan da ke mayar da su a matsayin kungiyar ’yan banga.
Sanarwar ta kuma yi zargin cewa ‘yan bindigar na dauke da bindiga AK-47 da makamai sun harbe makiyaya 12 tare da jikkata wasu da dama.
Abin takaici, kungiyar ta koka kan yadda ta’addancin ya faru kwanaki hudu bayan da aka kwace wasu makiyaya biyu da karfin tsiya daga hannun ‘yansanda tare da kashe su a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
Kungiyar ta yi nadama da cewa abin tsoro ne ganin yadda kashe-kashen da ake yi a halin yanzu ba wai kawai ya faru ba ne, inda ta jaddada cewa, misali ne kawai na tsawon shekaru na yadda ake ci gaba da kawar da su, da halaka, da kuma kawar da kabilanci da ake yi wa al’ummar Fulani makiyaya a jihohi daban-daban na tarayya.