Kungiyar gamayyar gidajen rediyo da talabijin na kasashen Afirka (URTNA) ta gudanar da bikin ba da kyautukan karramawa ga kafofin yada labarun kasashe daban daban, a Abidjan na kasar Kodibuwa, a jiya Juma’a, inda shirin musamman da babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG ya tsara, game da kaurar da dabbobi suka saba yi a gabashin Afirka, ya samu lambar yabo a fannin cudanyar al’adu da kirkiro sabbin fasahohi.
Kungiyar URTNA ta gudanar da taronta na shekara-shekara karo na 16 ne a birnin Abidjan, tsakanin ranekun 19 da 20 ga watan da muke ciki, inda bikin mika kyautukan yabon ya kasance wani muhimmin biki da ya gudana a karshen wa’adin taron. Kana a wajen bikin, ministan harkar watsa labarai na kasar Kodibuwa Amadou Coulibaly, a madadin URTNA, ya mika kyautar yabo ga wata wakiliyar kamfanin CMG.
Kafin haka, yayin da William Ruto, shugaban kasar Kenya, ke ziyara a kasar Sin a watan Afrilun bana, shi ma ya yabi CMG bisa gudunmowar da ya bayar ta fuskar karfafa cudanyar al’adu tsakanin kasarsa ta Kenya da kasar ta Sin.
A cewar shugaba Ruto, shirin talabijin da CMG ya tsara dangane da kaurar dabbobi a gabashin Afirka ya nuna muhallin halittu mai kyan gani na Afirka, wanda ya taimaka wajen janyo hankalin ‘yan yawon shakatawa na kasashe daban daban zuwa ga kasar Kenya. (Bello Wang)