Kungiyar Hisbah reshen karamar hukumar Katsina ta koyar da mambobinta guda 50 fasahar sadarwa na zamani, domin inganta rayuwarsu da kuma ta al’umma a fannoni daban-daban.
Horon wanda ya dauki watanni uku ana yin sa ya zo karshe a lokacin bikin yaye daliban wadanda aka raba wa shaidar kammala wannan horo a sassa daban-daban.
Tun da farko da yake jawabi, shugaban sashin fasahar sadarwa na zamani (ICT) na kungiyar Hisbah ta kasa, Malam Aminu Aliyu Albani ya yi bayanin muhimmancin koyon irin wadannan ayyuka domin dogaro da kai da kuma taimakon al’umma wanda aka san Hisbah da shi.
Ya ce mutum 50 aka fara da su, kuma za a ci gaba wajen fadada horon daga mambobin Hisbah na karamar hukumar Katsina zuwa wasu kananan hukumomi saboda amfanin da ke cikin wannan ayyuka.
Ya ce, “Mun yaye dalibai 50 kan daukar hoto da bidiyo da daukar sauti da wadanda suka samu horo a bangaren na’ura mai kwakwalwa, wanda suka hada da maza da mata, ” in ji shi.
Shi ma da yake nasa jawabin, shugaban Hisbah na karamar hukumar Katsina, Malam Shamsu Kabir ya gode wa wadanda suka taimaka wajen shirya wannan horo, inda ya ce an yi abin da ya dace kuma ya zo a daidai lokacin da ake bukatar hakan.
Ya kara da cewa wannan horo da suka samu su yi amfani da shi ga al’umma, kuma zai taimake su wajen yin aiki ko da kuwa na gwamnati ne saboda ingancin horon da suka samu.