Yanzu haka shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yana ganawa da hafsoshin tsaro da ministoci a fadar shugaban kasa a safiyar yau Juma’a.
Taron yana da nasaba ne da fasa gidan yarin Kuje inda fursunoni sama da 600 suka tsere ciki har da ‘yan Boko Haram.
Wadanda suka halarci taron sun hada da hafsoshin tsaro, sufeto janar na ‘yan sanda (IGP) da kuma ministocin harkokin cikin gida da na harkokin ‘yan sanda, tsaro, da shari’a.
Talla