Kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta kasa ta yaba wa hukumar sojojin Nijeriya wajen zantar da hukunci na korar sojojin da ake zirgi da kashe Sheikh Goni Aisami a kwanakin baya a garin Gashua ta Jihar Yobe.
Shugaban JIBWIS, Sheikh Abdullahi Bala Lau, shi ya yi wannan furuci a wata takarda da aka raba wa manema labarai a Kaduna.
- Kudin Da NNPC Ke Kashewa A Tallafin Mai Ya Wuce Kima – Hamid Ali
- Mace Za Ta Iya Yin Limancin Sallah?
Shehin malamin ya ce “Za mu ci gaba da bibiyar shari’ar da za ta gudana a kotu, domin ganin an tabbatar an yi musu hukuncin da ta dace da su a hukumance.
“Mun yaba da hukuncin da hukumar soji ta yi wajen gaggauta kwace mukamansu tare da korar su daga aiki cikin kankanin lokaci.
Wannan kungiya mai albarka a kullum takan yi kira ga mabiyanta a kan su zauna lafiya, kuma ba za mu zuba ido ana kashe malamanmu da dai-dai da dai-dai ba.
Har yanzu ciwon da aka mana na kisan Marigayi Sheikh Ja’afar da Marigayi Sheikh Auwal Albani ba mu warke ba, ga kuma na Sheikh Goni Aisami ya zamar mana sabo fil.
“Muna kira ga hukuma da ta din ga daukan mataki ga makasan in an kama su, wannan shi zai kawo karshen wannan ta’addanci ga malamanmu a fadin kasar nan, in ji Bala Lau.