Kungiyar marubuta kare hakkokin Dan’adam ta Nijeriya (HURIWA) ta yi tir da matakin gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Nasiru el-Rufa’i na korar malaman makarantu da ta yi, inda ta bayyana hukuncin a matsayin daukar fansa ba bisa ka’ida ba kuma abin Allah wadai.
Malaman da aka kora sun hada da shugaban kungiyar malamai ta kasa (NUT), Audu Amba, wanda aka kora bisa zargin kin yin jarabawar cancanta da hukumar ilimin bai-daya ta jihar (KADSUBEB) ta shirya.
HURIWA ta goyi bayan shugaban kungiyar NUT na jihar wanda tun da farko ya bayyana korar malaman a matsayin haramtacce.
Kungiyar kare hakkin ta ce matakin korar malamai a jihar ya saba wa sashi na 42 na kundin tsarin mulkin kasa, domin a cewar kungiyar, “Gwamnan da yake ma’aikacin ne a jihar da wadanda ya nada ba a yi musu irin wannan gwajin cancantar ba, sai a kan malamai, tabbas akwai nuna wariya,” in ji kungiyar.
Hakazalika, shi ma dan takarar gwamnan Jihar Kaduna na jam’iyyar PDP, Isah Ashiru Kudan, ya yi kira ga gwamnan Nasir el-Rufa’i ya dakatar da korar ma’aikatan da yake yi a jihar ba tare da bata lokaci ba.
Isah Ashiru ya soki hakan ne a cikin wani sako da ya fitar, inda ya ce a wannan lokaci da talaka ke hannu-baka-hannu- kwarya bai kamata a ce an gallaza masa da irin wannan azaba ta korar aiki da rana tsaka ba.
Ya ce ana fama da talauci da wahalhalun rayuwa sai kuma a wayi gari dan aikin da talaka ke samun abinci an kore shi, wannan rashin imani ne.