Kungiyar kawance ta Sin da Niger, ta bayyana goyon bayanta ga manufar Sin daya tak a duniya, cikin wata sanarwar da ta fitar a baya-bayan nan, dangane da ziyarar da kakakin majalisar wakilan Amurka, Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan.
Cikin sanarwar, kungiyar ta ce, ziyarar da kakakin majalisar wakilan Amurka ta kai yankin Taiwan, ta yi watsi da adawa mai karfi da korafin da Sin ta gabatar, lamarin da ya keta manufar Sin daya tak a duniya.
A cewarta, kasar Sin daya ce kadai ke akwai a duniya, kuma Taiwan, wani bangare nata ne da ba zai iya ballewa ba. Kana gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, ita ce halastacciyar gwamnati dake wakiltar baki dayan kasar Sin, wanda kudurin MDD mai lamba 2758 ya fayyace.
Kungiyar ta kara da cewa, yanzu haka, wasu kasashe a duniya na fuskantar rikici, kuma ana ci gaba da fama da matsalar lafiya da annobar COVID-19 ta haifar.
Sannan, duk da wadannan matsaloli, Pelosi ta nuna halin ko in kula wajen ziyartar Taiwan, lamarin da ba karan tsaye ga kokarin Sin na ganin dunkulewar yankunanta wuri guda kadai zai iya yi ba, har da illata dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka da ma dangantakar Sin da kawayenta.
Bugu da kari, sanarwar ta ce, kungiyar za ta kasance tsintsiya madaurinki daya da kawayenta Sinawa.
Kuma a matsayinta na mambar hadakar kungiyoyin kawancen Sin da Afrika, tana mara baya ga sanarwar Dakar ta ranar 4 ga watan Augusta, wadda ta yi kira ga Amurka da ta kai zuciya nesa, ta kuma girmama kudurin nan na MDD dake tabbatar da halaltattun hakkokin Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)