Kungiyar likitocin Nijeriya reshen jihar Kano (NMA) ta yi kira da a gaggauta dakatar da kwamishiniyar harkokin jin kai ta jihar, Hajiya Amina Abdullahi, bisa zargin cin zarafin wata Likita.
Saboda haka, kungiyar ta bayar da wa’adin sa’o’i 48 ga gwamnatin jihar, inda ta yi barazanar dakatar da aikin jinya a asibitin kwararru na Murtala Muhammad idan har ba a biya musu bukatunsu ba.
- Tsadar Rayuwa: Gwamna AbdulRazaq Ya Amince Da Wani Tallafii Ga Ma’aikatan Kwara
- Habasha Ta Shirya Taron Karawa Juna Sani Karo Na 1 Don Bunkasa Aikin Koyar Da Sinanci
NMA, a wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta, Dr. Abdurrahman Ali, da sakatarenta, Dr. Ibrahim D. Muhammad, ta bayyana cewa, lamarin ya faru ne a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2024 a sashin kula da kananan yara na gaggawa da ke asibitin.
Sanarwar ta ce, kwamishinar tare da tawagarta da jami’an tsaro sun ci zarafin likitan ne saboda rashin samun kayayyakin aikin da dole ana bukatarsu a ko da yaushe.
NMA ta kafa uzurin cewa, likitar tana kula da marasa lafiya fiye da 100 kuma ta ce lamarin ya sha karfinta.
Kungiyar ta kuma yi kira ga Gwamna Abba Yusuf da ya sa baki cikin gaggawa, inda ta yi gargadin cewa, rashin biyan bukatunsu na iya haifar da cikas a harkar kiwon lafiya a jihar.