Ma’aikatan Majalisar Dokokin Nijeriya (PASAN) ranar Talata sun janye yajin aikin da suka tsunduma na tsawon mako guda domin nuna fushi kan rashin samun alawus-alawus dinsu.
Wasu rahotanni sun tabbatar mana da cewa, mambobin PASAN din sun tafi yajin aikin kan rashin biyansu albashi mafi karanci da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ayyana da wasu batutuwan da suka shafi alawus-alawus dinsu.
- Lawan Na Fuskantar Barazanar Rasa Kujerarsa Wanda Ya Maye Gurbinsa Ya Ki Janye Masa
- Abun Mamaki: Lawan ya Manta Da Wasikar Murabus Din Abaribe A Gida
A cikin ranakun da ma’aikatan suka yi su na yajin aiki, sun rufe Majalisar gaba daya a rana ta biyu tare da kashe na’urorin hasken lantarki da sauran kayan amfani na Majalisar duka don nuna fushi kan lamarin.
Shugaban na PASAN, Sunday Sabiyi, shi ne ya sanar da matakin janye yajin aikin bayan cimma wata matsaya da shugabannin majalisar.
Sai dai PASAN ta yi barazanar sake tsunduma wani yajin aikin matsawar Shugabancin majalisar ya gaza aiwatar da abin da suka cimma daga nan zuwa karshen watan Yuli.