DAKTA FAUZIYYA BUBA IDRIS ita ce mataimakiya ta musamman ga Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan harkokin Lafiya, babbar jakadiya ga kokarin Mai Dakin Gwamnan Kano Farfesa Hafsat Ganduje wadda ke jagorantar gangamin kaddamar da dakarun Mata masu yaki da shaye-shayen Miyagun Kwayoyi a Kano.
Dakta Fauziya gogaggiyar likitar Mata ce sannan ‘yar siyasa mai rajin inganta rayuwar Mata da Kananan Yara.
A tattaunawartar ta Wakilinmu a Kano ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, Dakta Fauziyya ta jinjina wa kokarin Mai Dakin Gwamnan Kano bias kyakkawar kulawar da take bai wa Harkokin Mata da Kananan Yara, ta kuma bayyana bukatar kowa a cikin al’umma su kawo nasu gudummawar don ganin an kawo karshen shaye-shayen miyagun kwayoyi a Jihar Kano. Ga dai yadda tattaunawar ta Kasance:
Za muso jin wanda muke tare da ita a halin yanzu
Sunana Dakta Fauziyya Buba Idris mashawarciya ta musammana kan harkokin lafiya ga Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, sannan kuma jagorar aiwatar da kudurin Mai Dakin Gwamna Farfesa Hafsat Ganduje na kaddamar da dakarun yaki da shaye-shaye Miyagun Kwayoyi a fadin kananan Hukumomin Jihar Kano 44
Mene dalilin kokarin samar da dakarun Mata wadanda za su yi aiki wajen dakile matsalar shaye -shayen Miyagun Kwayoyi a tsakanin matasa?
Alhamdulillahi kullum Mai Dakin Gwamna damuwarta shi ne ta ga yara Mata da maza na kara tsunduma cikin wannan mummunar ta’ada, wannan ta sa ta yanke shawarar samar da dakarun Mata domin iyaye mata suke galabaita da wannan matsala domin su ake bari da dawainiya da yara a gida ko makarantu. Saboda haka ta kirkiri wannan aiki wanda zuwa yanzu mun kusa kamala karade Kananan Hukumomin Jihar Kano 44 tare da kaddamar da wadannan da karu.
Mene ayyukan wadannan dakaru?
Aikinsu shi ne shiga cikin gidaje domin fadakar da iyaye Mata illar ta’ammali da Miyagun Kwayoyi, sannan kuma mace tafi kowa sanin matsalar ‘yar uwarta mace, wadannan dakaru na da karfin guiwar tunkarar kowacce uwa da aka hangi danta a ciki masu irin wannan matsala kuma a yi mata gargadi tare da wayar da kanta domin kara himma wajen Lura da mu’amalar yaranta sannan kuma an samar da tsare-tsare na fadakar da duk wanda yantsunci kansa a irin wannan matsala.
Mene kuke ganin na kara ta’azzara wannan matsala tashaye-shaye?
Daga ciki akwai matsalar rabuwar iyali, muna nan abokai, damuwa, talauci da sakacin Iyaye, wadannan na cikin abubuwan da ke kara rura wutar matsalar shaye-shayea tsakanin matasa. Sai Kuma rashin samun ingantaccen Ilimi da kulawar iyaye.
Dakta kasancewar ki Mace kuma likita sannan gashi kina zaman mashawarciya ga Gwamna kan Harkokin Lafiya, shin ko ya kike kallon matsalar da a halin ake fuskanta na shigar Mata har ma da matan aure cikin matsalar Shaye-shayen miyagun kwayoyi?
Gaskiya wannan lamari ne mai tada hankali, kuma shi Mai Dakin Gwamna Farfesa Hafsat Ganduje ta kalla kuma ta himmatu wajen neman hanyar magance matsalar, Alhamdulillahi Jihar Kano mun yi dacen Gwamna wanda kullum damuwarsa ita ce ya za a Inganta rayuwar al’umma, wannan tasa shi ne Gwamna daya tilo da ya fara zartar da dokar dole duk wani mai neman takara ko nadi a mukamin Gwamnati sai an gwada kwakwalwarsa, kuma yanzu kowa ya Fara ganin tasirin wannan kokari na Gwamna Ganduje.
Ana samun yawaitar kwararar masu tallace-tallacen maganunuwa a kan Tituna da kasuwanni, wanda a lokuta da dama suke yin amfani da wasu kalmomi da ba su dace da harshen Hausa da al’adun mu ba Kai har ma da addini, shin ko akwai wannan matsala?
Babu shakka tuni wannan Gwamnati tare da hadin kan Ma’aikatar Lafiya Gwamnati ta bijiro da wasu dokoki ga duk wanda ke bukatar tallan Maganin Gargajiya ko makamancinsa, sannan dole mutum ya je a tantance shi tare don yi masa rijista, sannana na shirya masu taron bita lokaci zuwa lokaci domin kara samun wayewa da kwarewa ta fuskar sana’arsu.
Wane kira za ki yi musamman ga matasa a lokaci irin wannan da aka fara kada kugen siyasa?
Daman tuni Gwamna ya ja kunnen Jama’a musamman ‘yan Jam’iyyar APC cewar kar wanda ya bari aka yi amfani da shi wajen tunzura matasa ko amfani da kayan maye ko makamai a lokacin yakin Neman Zabe, wannan tasa yanzu matasa a Kano an daina tunzura su aikata bangar siyasa.
Mun gode kwarai da gaske
Ni ma na gode