Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta sanar da dakatar da kiwo da dadaddare da hana yara shiga harkar kiwo a Jihar Kwara. Wannan sanarwar ta fito ne daga Shugaban MACBAN na ƙasa, Alhaji Baba Othman-Ngelzarma, a lokacin kaddamar da sababbin shugabannin ƙungiyar a Ilorin, babban birnin jihar.
Othman-Ngelzarma ya bayyana cewa wannan matakin na nufin inganta zaman lafiya da haɗin kai tsakanin makiyaya da manoma a jihar, tare da kaucewa rikici kan amfani da filayen kiwo da na Noma. Ya yi gargaɗi cewa duk wanda aka samu yana kiwo da dabbobi da da daddare zai fuskanci hukunci mai tsanani, har da miƙa shi ga hukumomin tsaro.
- Kungiyar Fulani Ta MACBAN Ta Nesanta Kanta Daga Zanga-zangar Matasa
- Tsadar Sufuri: Jihar Kwara Ta Kaddamar Da Sufuri Kyauta
Sabon shugaban MACBAN na Jihar Kwara, Alhaji Idris Abubakar, ya tabbatar da cewa ƙungiyar za ta tabbatar da bin wannan doka don ci gaba da tsare zaman lafiya da kuma rayuka tsakanin al’ummomar jihar.