A kwanakin baya ne kuniyar zauren al’ummar Hausawan Duniya, cikin bukuwan ranar Hausawan Duniya ta kai wa Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ziyara, tare da zabarsa a matsayin uban wannan kungiya.
Cikin jawabinsa na maraba, Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ya nuna godiyarsa ga Allah ya ba da ikon kabar bakuncin wadannan baki nasa.
- Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Keta Ka’idojin Fitar Da Kayayyaki
- Wani Abun Fashewa Ya Tarwatse A Wani Masallaci Ya Kashe Akalla Mutane 18 A Afganistan
Mai Martaba Sarki ya ce, “muna mika matukar godiyar mu ga Allah da ya ba mu ikon ganin wannan rana cikin koshin lafiya har muka karbi bakuncin ku.
Muna godiya ga Allah da ya kawo ku lafiya, tate da fatan za ku koma lafiya.”
Haka kuma Sarkin ya nuna farin cikinsa da zabarsa da aka yi a matsayin Uba na wannan kungiya ta Zauren al’ummar Hausawan Duniya, “ba abin da za mu ce sai dai Allah saka maku da alhairi,” in ji Sarki.
Ya ci gaba da bayyana cewa saboda muhimmancin wannan rana da kuma al’ummar Hausan Duniya, “ya zama wajibi a gare mu mu karbi wannan girma da aka dora mana.
Tare da fatan Allah zai mana ludufi ya ba mu ikon dauka,” In ji Sarkin na Zazzau.
Cikin zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan kammala wannan ziyara, Shugaban zauren Hausa ta duniya, Ambasada Muhammad Kabir Gure ya bayyana cewa sun zabi kawo wannan ziyara a wannan rana ce domin muhimmancin ranar, wacce ya ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware don Hausan duniya.
“Wannan muhimmiyar rana ce a gare mu, shi ne muka kawo wa Mai martaba Sarkin Zazzau ziyara domin ya sanya mana albarka.
Kuma a matsayinsa na Uba, ya sa mu ka zo neman albarka, wanda kuma a yanzu haka mun ba shi matsayin Uba na wannan kungiya,” in ji Ambasada.
Alhaji Sanusi ya kara da cewa a halin da ake ciki, Bahaushe bai isa ya tashi ya yi doguwar tafiya cikin kwanciyar hankali ba, “saboda haka sai muka ga ashe ke nan ba biki ya kamata mu yi ba, alhini za mu nuna, ai ranar bikinmu, ita ce ranar da ‘yan uwanmu suka fito daga daji,” in ji shi.
Ya ce, wannan ne ya sa suka zo wurin mai martaba Sarkin Zazzau domin jajanta wa juna, tare da yin kira ga gwamnati ta hanzarta karbo mutanenmu da ke dazuka.