Manya da kananan kungiyoyin kwallon kafa dake buga babbar gasar Firimiya ta kasar Ingila sun kashe makudan kudade wajen daukar sabbin yan wasa yayin da aka fara sabuwar kakar wasa ta bana, inda aka kiyasta kudin da aka kashe sun kai Yuro Biliyan 3 kwatankwacin Dala Biliyan 4 a kasuwar musayar yan kwallo, masana sun bayyana cewar wannan ya kara tabbatar da gasar Firimiyar a matsayin mafi girman gasar kwallon kafa a duniya.
An rufe kasuwar a daren ranar Litinin lokacin da Liberpool ta sanar da sayen dan wasan gaba na Newcastle Aledander Isak kan kudi Fam miliyan 125 bayan shafe tsawon lokaci ana kai ruwa rana kan daukar dan wasan na kasar Sweden, jimillar kudaden da aka kashe a wannan kakar ya karu da kusan Fam miliyan 650 sama da na baya na Fam biliyan 2.4 da aka kashe a shekarar 2023, a cewar Deloitte.
- Al Hilal Za Ta Biya Yuro Miliyan 53 Don Ɗaukar Nunez Daga Liverpool
- Liverpool Za Ta Kece Raini Da Bournemouth, Arsena Za Ta Bakunci Man Utd A Wasan Mako Na Firimiya Ta Baɗi
Wannan dai shi ne karo na uku a jere a lokacin rani wanda yawan kudaden da aka kashe ya zarce Fam biliyan biyu, kuma na farko da ya kai Fam biliyan uku, yayin da Ingila ta samu yawan wakilai a gasar Zakarun Turai ta bana fiye da kowane lokaci da suke fafatawa a gasar ta Turai, kungiyoyin na Firimiya suna neman jan hankalin yan wasa da kuma kara tabbatar da gasar a matsayin gasa mafi girma a fagen kwallon kafa a Duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp