Kungiyar Likitoci ta Nijeriya, NARD, ta fara gudanar da yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai, kan garkuwa da Dakta Popoola Ganiyat, a jerin gidajen ma’aikatan asibitin kula da lafiyar Ido ‘National Eye Center’ da ke Kaduna, watanni takwas da suka gabata.
Mataimakin shugaban kungiyar NARD a shiyyar Kudu maso Gabas, Dokta Egbue Obiora, ya shaida wa LEADERSHIP cewa, yajin aikin gargadin an fara ne a ranar Litinin, amma za a sake duba matakin nan da kwanaki bakwai.
- Sanata Bomai Ya Bada Tallafin Miliyan 20 Da Tufafi Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Yobe
- Kasashen Duniya Sun Halarci Baje Kolin Mutum-mutumin Inji Na Duniya
An yi garkuwa da Dakta Ganiyat ne tare da mijinta da kuma dan dan’uwanta a ranar 27 ga Disamba 2023.
Bayan ƙoƙari da tattaunawa, masu garkuwar sun saki mijinta a ranar 8 ga Maris 2024, sannan suka sake gabatar da sabbin buƙatu domin sako sauran biyun da ke tsare a wurinsu.