An samu kura-kurai masu dimbin yawa a lokacin gudanar da zaben gwamna a jihohin Kogi, Imo da Bayelsa a ranar 11 ga Nuwambar 2023.
Masu sa ido a zabukan sun bayyana yadda tashe-tashen hankula da sayan kuri’u da sauran nau’o’in magudi sunka turnike zabekan a dukkan jihohin guda uku.
- Zaben Kogi: INEC Ta Musanta Zargin Sauya Kuri’un Da Ta Dora A Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe
- San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
Sai dai kuma hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran hukumomin tsaro sun samu nasarar damke mutane da dama wadanda ake zargi da sayan kuri’u da kitsa tashe-tashen hankula a lokacin zabukan.
Haka kuma an samu tangardan na’uran wajen tantance masu zabe da kuma saka sakamakon zabe. Sannan a wasu rumfuna da dama ba a samu nasarar kai kayayyakin zabe da wuri ba, wanda yakan ya kawo tsaiko wajen fara zabukan kamayar yadda aka tsara.
A cikin rahoton kungiyoyin masu saka ido a zabuka, sun bayyana cewa ‘yan siyasa da dama sun karya dokokin zabe a jihohin Kogi, Imo da Bayelsa, wanda suka dunga sayan kuri’u da kuma haddasa tashe-tashen hankula domin su samu damar cimma burikansu na siyasa.
Shugabannin kungiyoyin karkashin jagorancin, Dakta Asmau Maikudi da Cynthia Mbamalu sun ce a ranar zabukan an samu tangardar na’ura wajen tantance masu zabe da kuma tura sakamakon zabe a kananan hukumomi masu yawa da ke jihohin guda uku.
A cewar rahoton masu saka idon, rumfuna da dama a zabukan an tantance mutane ne ba tare da na’ura ba kamar yadda dokar zabe ta tanada, wanda hakan ya kawo yin magudi da kuma karya dokokin zabe.
Sun dai yi kira da a gaggauta kame wadannan ‘yan siyasa da kuma jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), wadanda suka kada kai da ‘yan siyasan wajen yin magudi.
“Mun yi matukar damuwa yadda aka dunga tantance masu zabe ba tare da na’urar ba, wanda yakan ya hassasa hanyar yin masudi da sauran hanyoyin karya dokokin zabe a jihohin Kogi, Imo da kuma Bayelsa.”
Masu saka idon sun yi Allah wadai da yadda aka yi garkuwa da babban jami’in hukumar INEC a karamar hukumar Sagbama, inda suke kira da a gaggauta sako shi tare da cafke wadanda suka aikata mummunan aikin.
Rahoton masu saka idon ya bayyana cewa kashi 65 na rumfunan zabe a Bayelsa aka fara zabe da wuri, yayin aka samu kashi 80 a Jihar Imo, sabanin a Jihar Kogi da aka samu na kashi 40 wurin fara zabe a kan lokaci.
Rahoton ya ce an samu rashin fitowar masu jefa kuri’a a wasu rumfuna, inda a rumfa mai lamba ta daya da ke Orsu ta Jihar Imo, jami’an INEC sun fito tun da wuri, amma masu jefa kuri’a kalilan ne aka samu sun zo jefa kuri’a sakamakon fargabar tashin hankali.
A Jihar Bayelsa kuwa, rahoton masu saka idon ya bayyana cewa jami’an INEC da suka gudanar da zabe a rumfar ta 24 a Yenagoa, an fara zaben ne da misalin karfe 11: 37 na safe, yayin da a Oporoma da ke kudancin karamar hukumar Ijaw, jami’an INEC sun iso rumfar zaben ne da misalign karfe 12: 15, sannan a rumfa ta 10 da ke karamar hukumar Ogbia an fara zaben ne da misalin karfe 12: 40 na rana.
Haka kuma rahoton masu saka idon a Jihar Kogi ya bayyana cewa har zuwa karfe 10:54 ba a fara zabe a rumfunan zabe da ke Iluteju, Okesi, Okibo, Eni, Oshobeni da Aiyeronmi a karamar hukumar Ogori-Magongo.
A Jihar Imo ma an samu jami’an INEC da zuwa latti a mafi yawancin runfunan zabe da suka hada da Abu/Oforola, Ehime Mbano, Mbaitoli-Ezinihitie, Umuokpiriri, Umuogu, Arewacin Owerri da kuma Isiala Mbano. Rahoton ya ce sai da misalin karfe 10: 23 na safe ne aka fara gudanar da zabe a rumfunan zabe a
Ihitteoha da wasu rumfunan zabe da ke karamar hukumar Owerri ta Arewa.
Rahoton ya ce a dukkan jihohin guda uku an samu rahoton sayan kuri’a daga kan naira 5,000 zuwa 22,000 ga kowani mai kada kuri’a.
Sannan rahotanni sun bayyana cewa an samu satar akwatin zabe tare da farmakar jami’an INEC a lokacin gudanar da wannan zabuka.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta bayyana cewa ta samu nasarar damke mutum 14 da ake zargi da sayan kuri’u a zaben gwamna a jihohin Kogi da Imo da kuma Bayelsa.
Mai magana da yawun hukumar EFCC, Dele Oyewale shi ya bayyana hakan a lokacin tattaunawa da manema labarai kan zabukan gwamna a jihohin uku.
Ya ce an samu nasarar kwato jamillar kudade da suka kai naira 11,040, 000 da 9,310,00 da kuma 1,730,000 daga hannun masu sayan kuri’a a dukkan jihohin guda uku.
Hukumar EFCC ta ce za ta gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.
Jam’iyyar APC ce ta samu nasarar lashe zabe a jihohin Kogi da Imo, yayin da jam’iyyar PDP ta lashe zabe a Jihar Bayelsa.