Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta sama wa ‘yan Nijeriya gidaje guda 80,000 a cikin shekara 4.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin babban sakataren ma’aikatar gidaje da tsara birane na tarayya, Mamuda Mamma, a zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar koli na ma’aikatar karo na 12 wanda aka gudanar a Jihar Kaduna.
- Kotun Daukaka Kara Ta Ayyana Zaben Gwamnan Zamfara A Matsayin Bai Kammala Ba
- Kungiyar Kwadago Ta Janye Daga Yajin Aikin Da Ta Shiga
Mamman ya bayyana cewa gwamnati za ta kammala shirinta na gina gidaje masu saukin farashi wanda duk wani dan Nijeriya zai samu damar mallakar a duk inda yake a fadin kasar nan.
Ya kara da cewa gidajen na kowa da kowa ne, burin Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu shi ne, ya ga duk wani dan Nijeriya ya mallaki muhalli a cikin shekara 4 na zangon farko na gwamnatinsa.