Kwararru a fannin aikin noma sun zayyano wasu hanyoyin da ya kamata masu yin noma domin samun riba su rika amfani da su, don samun kai wa ga nasara a fannin kasuwancin noma.
Ga wasu daga cikin hanyoyin kamar haka:
Bisa bayanin wani kwararren mai fashin baki a fannin kasuwancin noman, Jonathan Ogwumike, ya bayyana cewa; fannin noma don samun riba a Nijeriya da kuma Afirka, ba wai magana ce ta tunanin yin kudi a cikin dan kankanin lokaci ba.
Ya kara da cewa, ana samun nasara a fannin ne kawai bisa jajircewa ta hanyar yin hakuri da kuma aiwatar da kyakkyawan shiri.
Haka zalika, Jonathan ya yi nuni da cewa, duba da irin yanayi na aikin noma; abu ne da ke bukatar isassashen lokaci kafin amfanin gona ya kammala girma, kana kuma a kai shi kasuwa don sayarwa.
“Wannan ya nuna cewa, fara cin gajiyar jarin da aka zuba a fannin, abu ne da zai iya shafe wata da watanni ko shekaru masu yawa. Sannan, ana son manomi ya kasance mai hakuri da dagewa har ya kai ga cimma burin da ya sa a gaba,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, ana so manomi ya ci gaba da kasancewa mai kwarin guiwa, sannan kuma ka da ya damu da abin da ya ji daga wurin wasu ko ya karanta, domin kuwa ba zai yiwu ya zama mai kudi a dare daya ba.
Kwaikwayon wasu: Akasarin wasu daga cikin manoma na yin noma don samun riba, kazalika suna kwaikwayon wasu ne daban. Amma bisa ka’ida, an fi bukatar manomi ya kirkiri wani abu da kansa da yake son ya yi, domin ba lallai ne kasuwancinsa ya yi iri daya da na wani ba.
Sai kuma batun yin kasuwanci ba tare da tsari ba: mafi yawan ‘yan kasuwa, ba sa tanadin wani tsari kafin su kai ga fara aiwatar da kasuwancin noma, ko kuma a kan burin da suke son cimma a fannin na noma domin kasuwanci.
Kazalika, ba sa yin wani tsari a kan yadda za su janyo ra’ayin abokan cinikayyarsu, don samar wa da kawunansu kudaden shiga masu yawa.
Rashin adana bayanan kasuwancin nasu: Rashin tanadar littattafan adana bayanan cinikayyarsu, wata babbar matsala ce a wannan fanni na kasuwancin noma, domin kuwa ba za ka iya hakikance ribar da ka ke samu a kullum ko a wata ba, wanda hakan ba karamin illa ya ke yi wa manomi ba.
Daukar ma’aikatan da ba su cancanta ba: Daukar ma’aikatan da ba su cancanta ba, wajen tafiyar da kasuwancinka ba karamar illa zai yi maka ba, domin kuwa wannan kasuwanci naka zai iya samun matsala ta kowace fuska. Saboda haka, ana so ka dauki kwararrun ma’aikata, wadanda za su rika sa ido sosai a kan bayanan harkokin kasuwancin naka.
Rashin sanya ido: Idan manomi yana son yin noma don ya samu nasara a kasuwancinsa, wajibi ne ya kasance yana sa ido sosai ta yadda zai tafiyar da kasuwancin yadda ya kamata.
Haka nan kuma, rashin daukar dabarun da suka dace: Wani kamfani mai suna SwagCo ya bayyana cewa, akasarin masu zuba jarinsu a noma don kasuwanci, ba sa daukar irin tsarin da ya dace wajen zuba jarin nasu a fannin.
Wanda kuma rashin daukar dabarun da suka dace din na sanya wadanda suka zuba jarin nasu a fanin yin asarar kudade masu daman gaske da kuma karancin samun riba. Saboda haka, ana so manoma su kasance masu samar da kyakyawan shirin da ya dace a kasuwancinsu.