• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN Ta Nuna Amincewar Jama’ar Da Sauye Sauyen Da Sin Ke Aiwatarwa

by Sulaiman and CGTN Hausa
1 year ago
Cgtn

Taro na uku na zaman kwamitin kolin JKS na 20 dake tafe na ci gaba da jan hankalin sassan kasa da kasa. Kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa sauye sauye daga dukkanin fannoni, da mayar da hankali ga yayata zamanantarwa irin ta Sin. 

Game da hakan, sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta Sin ta gudanar ya nuna cewa, kaso 76.9 bisa dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu, sun jinjinawa nasarar da Sin ta cimma a fannin samar da ci gaba mai inganci, kana suna fatan kara fadadar zurfafa sauye sauyen na Sin daga dukkanin fannoni zai samar da karin damammaki ga sassan duniya.

  • Noma: Gwamnan Zamfara Ya Nemo Masu Zuba Jari Daga Ƙasar Turkiyya
  • NPA Ta Kaddamar Da Kananan Jiragen Ruwa Don Saukaka Zirga-zirga A Matatar Man Dangote

Tun bayan babban taron JKS na 18, an aiwatar da manufofin sauye sauye da suka haura 2,000, wadanda suka shafi sassa daban daban na tattalin arziki, siyasa, raya al’adu, kyautata zamantakewa da kare muhallin halittu.

Yayin kuri’un na jin ra’ayin jama’a, kaso 80.3 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu sun bayyana gamsuwa da bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, suna masu imani da cewa hakan zai haifar da karin alfanu ga duniya baki daya. Yayin da kaso 93.2 bisa dari na masu bayyana ra’ayin suka jinjinawa karfin kwazon Sin a fannin raya ilimin kimiyya da fasaha. Sai kuma kaso 85.4 bisa dari da suka yabi nasarar da Sin ta samu ta fuskar kirkire-kirkire na kashin kai. Baya ga kaso 78.5 bisa dari da suka amince cewa, sassan masana’antu dake amfani da makamashi mai tsafta za su kara ingiza ci gaba mai inganci na kasar Sin.

Masu bayyana ra’ayoyi 15,037 daga sassa daban daban na duniya ne suka bayyana matsayarsu, ciki har da al’ummun kasashe masu sukuni da suka hada da Amurka, da Birtaniya, da Faransa, da Sifaniya da Australia, da kuma wasu kasashe masu tasowa irin su Brazil, da Thailand, hadaddiyar daular Larabawa, da Masar da Afirka ta Kudu. (Saminu Alhassan)

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
Daga Birnin Sin

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Daga Birnin Sin

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Next Post
Kungiyar Tsaro Ta NATO Ba Za Ta Iya Dora Alhakin Rikicin Ukraine Kan Kasar Sin Ba

Kungiyar Tsaro Ta NATO Ba Za Ta Iya Dora Alhakin Rikicin Ukraine Kan Kasar Sin Ba

LABARAI MASU NASABA

Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

November 6, 2025
Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

November 6, 2025
Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

November 6, 2025
Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.