Cutar kwalara ta ɓarke a ƙananan hukumomin Gumi da Bukkuyum a Jihar Zamfara, inda ta kashe aƙalla mutum bakwai tare da kwantar da kusan mutum 200 a asibiti.
Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar yankin, Hon. Sulaiman Abubakar Gumi, ya ce cutar ta fara tun 10 ga watan Agusta, kuma tana ƙara yaɗuwa.
- Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya
- Hukumar NRC Ta Dakatar Da Zirga-zirgar Jiragen Kasa Na Abuja zuwa Kaduna
Ya bayyana cewa rashin tsaftar muhalli da ruwan sama sun taimaka wajen yaÉ—uwar cutar, musamman a inda ‘yan gudun hijira suke zaune.
Ya yi gargaÉ—in cewa idan ba a É—auki matakan gaggawa ba, cutar na iya zama annoba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp