Cutar kwalara ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 25 a Jihar Sakkwato, inda ta shafi kananan hukumomin Sakkwato ta Arewa, Kware da Silame.
Kwamishinar Lafiya ta Jihar, Hajiya Rabi Balarabe ce, ta tabbatar da cewa mutum 1,160 ne suka kamu da cutar, yayin da 15 ke kwance a asibiti suna karbar magani.
- Babu Wata Kasa Da Za Ta Ce ”Ita Kadai Ta Isa Gayya”
- An Kashe Mutum 50, An Sace 170 Cikin Wata 7 A Kaduna
Matsalar ta fi tsanani a Bazza Gidadawa da ke Karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa.
Gwamnatin jihar ta samar da magunguna kyauta ga yankunan da abin ya shafa tare da daukar ma’aikatan jinya 864 don bunkasa bangaren lafiya.
Ana ci gaba da kokarin dakile annobar da tallafa wa al’ummar da abin ya shafa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp