Wani kwale-kwale da ke ɗauke da fasinjoji 20 ya kife a ƙauyen Nahuce, yankin ƙaramar hukumar Taura ta Jihar Jigawa, inda ake tsoron cewa a ƙalla mutane biyar sun mutu. Lamarin ya faru ne da yammacin yau Alhamis yayin da kwale-kwalen ke ketare kogin Gamoda. Ana ci gaba da neman a ruwa don kuɓutar da sauran fasinjojin.
Lawan Shiisu Adam, mai magana da yawun rundunar ‘Yansandan Jihar Jigawa, ya tabbatar da afkuwar wannan lamari, inda ya bayyana cewa ‘yan kogo, da Ƴansanda, da wasu mazauna yankin suna cikin ƙoƙarin ceto mutanen. Ya ce Ƴansanda sun samu rahoton faruwar wannan hatsari da misalin ƙarfe goma sha biyu na rana, kuma nan take suka tura wata tawaga don taimakawa aikin ceton. Sai dai kuma kash, an tabbatar da mutuwar fasinjoji biyar.
- Jami’an Tsaro Sun Yi Wa Ofishin NLC Dirar Mikiya Don Neman Hujja Kan Zanga-zangar Yunwa
- ’Yansanda Sun Cafke Karin Mutane 82 Kan Zanga-zangar Yunwa A Jigawa
Wannan mummunan lamari na zuwa ne bayan irin wannan haɗari da ya faru a watan da ya gabata a ƙaramar hukumar Auyo, inda wani kwale-kwale mai ɗauke da fasinjoji 20 ya kife a Kogin Kwalgwai, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu. Hatsarin da ya faru a baya an danganta shi da cunkoso da kuma tsananin ruwa.