Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da nutsewar dalibai biyu na Kwalejin Aikin Gona ta Audu Bako da ke karamar hukumar Makoda a wani Dam.
Kakakin hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren Laraba, ya ce lamarin ya shafi dalibai uku, amma ya ce an ceto wani mai suna Ibrahim.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda, Sun Ceto Mutane A Katsina Da Filato
- Kamfanin Sin Ya Bayar Da Tallafin Kayayyaki Ga Wadanda Ambaliya Ta Shafa A Kenya
A cewar sanarwar, “A ranar Talata 30 ga watan Afrilu, 2024, hukumar kashe gobara ta jihar da ke karamar hukumar Danbatta ta samu kiran agaji da misalin karfe 3:06 daga Kwamared Ibrahim Muhammad wanda ya sanar da faruwar lamarin.
“Bayan isa wajen, sun tarar da dalibai uku da ke karatu a Kwalejin Aikin Gona ta Audu Bako da ke karamar hukumar Makoda wadanda suka shiga kwale-kwale da niyyar tsallakawa, amma suka nutse.
“Cikin ikon Allah matukin kwale-kwalen ya yi nasarar ceto daya daga cikin daliban mai suna Ibrahim mai shekaru 21.”
Abdullahi ya kara da cewa jami’an hukumar da masunta a yankin sun yi nasarar ceto dalibai biyu; Abubakar Sanusi mai shekaru 22 sa Salisu Ado mai shekaru 21.
Ya bayyana cewa da fari an ceto daliban a sume, amma daga baya likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.
Abdullahi ya ce an kwantar da wanda ya kubuta a babban asibitin garin Danbatta, inda yake ci gaba da murmurewa.