Abaya dogon riga ne dake haska kwalliyan mata na yau da kullum. Abaya kwalliya ne da mata ke son shi mussamman a zamanin mu na yau saboda tufafi ne da ke rufe jikin diya mace daga sama har kasa harma da hannayenta.
Abaya ya samu asali ne daga kasashen larabawa wanda hakan ya bayyanar da kalmar Abaya. Inda matan larabawa ke kwalliyarsu dashi.
Abaya riga ce da musulmai ke amfani dashi a kasashen duniya wanda suke ganin shi ne mafi saukin kaya wajen rufe jikinsu gaba daya. Haka zalika wadanda ba musulmai bama sun kasance suna saka abaya saboda saukin shi da kuma kasan cewarsa kaya mara nauyi kuma kaya ne mai rufe tsiraicin jiki.
Abaya a yau ya zama tufafi daya zaga duniya gaba daya wanda har a kasarmu ta Nijeriya an dauketa a matsayin tufafi na mutunci da kuma kamala domin yadda ya kasance abin rufe jiki ga mata.
Abaya dogon riga ne wanda ake kawatashi da kwalliya, wasu na da duwatsu wasu na da zubin zare wasu kuma plain.
Abaya yawancinsu bakine amma kwalliya irin na zamani yasa akwai wasu launika daban daban wanda ake kira da Arabian gown. Amma dai Abaya ya kasu kala daban daban akwai wanda ake kira ‘After dress’ wanda ake sawa indan an saka kaya na musamman a ciki ko kana nan kaya sai a daura shi akai.
Akwai kuma dogon riga wanda gaban a rufe yake ba kaman ‘after dress’ ba, shi ana saka shi ne a matsayin riga mai zaman kanshi.
Sai kuma Arabian gown wanda shima kaman Abaya yake kawai shi azamanin mu na yau yazo da ‘styles’ nashi da launika daban daban yasa mutane ke kiran kayan da arabian gown. Abaya a zamanin mu na yau akwai din kuna da ban da ban.
Akwai wanda ake yin shi mai dinkin fuka fukai wato dinkin irin na ‘butterfly’ wanda ake kira da malam bude takarda.
Akwai wanda yake dogo mai ‘shape’ wasu kuma suke kara saka shape din don ya kara kawata kayan da kwalliyan su. Daga sama ‘shape’ din yake kasan kuma yake abude. Akwai wanda ake yi masu belt mai fadi ko siriri.