Hukumar gudanar da gasar Firimiyar Najeriya, ta dakatar da shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Yahaya Surajo, saboda naushin mataimakin alkalin wasa a lokacin wasan mako na 31 da kungiyar ta kara da Dakkada FC a Kano a ranar Alhamis.
A cikin wani faifan bidiyo ne, a ka ga Surajo, ya kai wa wani mataimakin alkalin wasa naushi yayin da ake tsaka da wasa, lamarin da kungiyar ta bayyana a matsayin abin takaici, wanda ba za ta aminta da shi ba.
- Masana Sun Gano Kaifin Basirar Kurege Wajen Rashin Mantuwa
- Mahara Sun Kai Hari Ofishin ‘Yan Sanda A Kogi
“Don haka kungiyar masu kungiyoyin kwallon kafa din ta dakatar da shugaban kungiyar ta Kano Pillars, Malam Yahaya Surajo daga dukkan ayyukan kungiyar har zuwa lokacin da za a gudanar da cikakken bincike kan lamarin,” Alloy Chukwuemeka, Sakataren zartarwa na kungiyar”, in ji sanarwar.
Shugaban kungiyar Barr. Isaac Danladi, ya ce ciyaman din na Kano Pillars zai fuskanci kwamitin ladabtarwa don kare kansa kafin a sake shigar da shi cikin kungiyar.
Kano Pillar ta sha fuskantar hukunci daga hukumar gudanarwa ta gasar Firimiyar Najeriya (LMC), wanda a baya-bayan nan magoya bayanta sai da suka farfasa motar kungiyar kwallon kafa ta Katsina United a Kano.
Lamarin da ya sanya aka kwashe mata maki, tare da sauya mata filin gudanar da wasa zuwa filin wasa na MKO Abiola da ke birnin tarayya Abuja.