Kwamishinan ƴansanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Bakori, ya karrama jami’ai 29 da aka kara wa matsayi, yana mai jan hankalinsu da su ci gaba da aiki da kwarewa, ladabi da gaskiya wajen aiwatar da aikinsu.
Yayin bikin karramawar da aka gudanar a Officers’ Mess ranar Litinin, CP Bakori ya bayyana ƙarin girman a matsayin sakamakon jajircewa da biyayya ga aiki, tare da yabo ga Hukumar Kula da Ayyukan Ƴansanda (PSC) bisa amincewa da ƙarin girmn, bayan shawarwarin da Sufeton Ƴansanda na Ƙasa, Dr. Kayode Egbetokun, ya bayar.
- Yadda Ƴan Agbero’ Ke Cin Karensu Ba Babbaka A Abuja
 - Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe
 
Ya ƙara da godiya ga AIG Zone 1 Kano bisa jagoranci da goyon bayan da yake bai wa rundunar, wanda ya ce ya taimaka matuka wajen inganta tsari da aiki a shalƙwatar ƴansanda ta Nijeriya (NPF). A cewar sa, jami’ai biyu an musu ƙarin girma daga CSP zuwa ACP, sai kuma 21 daga SP zuwa CSP, sannan 6 daga DSP zuwa SP.
CP Bakori ya tunatar da sabbin jami’an cewa karin matsayi ba wai kyauta ba ne, illa dai sabuwar alhakin jagoranci. Ya bukace su da su zama abin koyi, su jagoranci da gaskiya tare da inganta hadin kai da dabarun aiki don magance matsalolin tsaro da ke fuskantar kasa.
A karshe, kwamishinan ya tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda a Kano za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya, tare da tabbatar wa jama’a da cewa ana daukar duk matakan da suka dace don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
			




							








