Kwamishinan ‘Yan Sanda.’n Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya roƙi sarakunan gargajiya musamman masu unguwanni da su taimaka wajen yaƙi da faɗan daba da sauran miyagun laifuka a tsakanin al’umma.
Ya yi wannan kira ne a taron masu ruwa da tsaki da aka shirya a filin wasa na Sani Abacha, wanda kwamitin daƙile matsalolin tsaro na jihar ya shirya.
- Yaƙin Neman Zaɓe A 2027: Ƙungiya Ta Nemi A Maye Gurbin Mai Magana Da Yawun Shugaban Ƙasa
- Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Yi Watsi Da Matsawa Sauran Kasashe Lamba
CP Bakori, ya ce sarakunan gargajiya suna da muhimmanci matuƙa wajen taimaka wa ‘yansanda gano matsalolin tsaro a unguwanni da kuma magance su.
Ya buƙaci su riƙa haɗa kai da jami’an ‘yansanda na yankinsu domin magance duk wata matsala tun kafin ta zama babba.
Kwamishinan ya bayyana cewa kafa kwamitin ya taimaka sosai wajen haɗin gwiwar hukumomin tsaro, wanda hakan ya ba su damar yin aiki tare da samun nasarori.
Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata.
Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa.
Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne a bai wa matasa damar samun ilimi, koyon sana’o’i da kuma wasu ayyuka da za su riƙa shagaltar da su zuwa hanya mafi dacewa.
Ya kuma shawarci shugabannin ‘yansanda na ƙananan hukumomi da su riƙa haɗa kai da sarakunan gargajiya da al’ummar yankinsu wajen gano matsalolin tsaro a yankunansu.
“Idan muka haɗa kai da goyon bayan jama’a, babu yadda ‘yan daba za su ci gaba da addabar Kano,” in ji CP Bakori.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp