Kwamitin haƙar ɗanyen mai na hukumar tattara kuɗaɗen shiga da hada-hadar kuɗi (RMAFC), ya koka da jinkirin da ake samu wajen aiwatar da aikin haƙar ɗanyen man fetur a Kolmani wanda kamfanin Integrated Oil, ke yi da aka fara shekaru biyu bayan ƙaddamarwa.
Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ziyarar duba matakin da ake kan aikin, kwamishinan gwamnatin tarayya na RMAFC, Injiniya. Hassan Mahmoud, wanda shi ne muƙaddashin shugaban kwamitin ɗanyen mai, ya ce ziyarar ta zama wajibi saboda gano man a wurin wanda zai taimaka matuƙa wajen samun kuɗaɗen shiga ga ƙasa.
- Man Girki Mara Asali: Kamfanin Power Oil Ya Kulla Alaka Da Ali Nuhu Kan Wayar Da Kai
- Gwamnan Gombe Ya Aza Tubalin Gina Majalisar Dokoki Da Babbar Kotun Jiha Na Zamani
Injiniya Mahmoud, ya nuna takaicin kan alaƙar kamfani Sterling Global, da al’ummar yankin na samar musu da ci gaba wanda tun shekaru biyu da suka gabata tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya ƙaddamar da aikin haƙo man na Kolmani, kuma shi ne na farko a Arewacin Nijeriya.
Kamfanin mai na NNPCL, tare da haɗin gwuiwar kamfanin New Nigeria, sun gano rijiyoyin mai guda biyu da suka wa laƙabi da OPL809 da kuma OPL810, a garin Kolmani, wanda aka yi hasashen za a samu kusan ganga biliyan ɗaya na ɗanyen mai kuma ana sa ran zai ɗore har zuwa shekarar 2060 inda NNPC, ya sha alwashin ci gaba da aikin amma a yayin ziyarar ba a ga alamar hakan ba.
Ɗya daga cikin injiniyoyin kamfanin Sterling Global, Abdulhamid Aminu, ya ce suna ƙoƙarin haƙar a rijiyoyin guda biyu na PL809 da OPL810 da aka gano kafin a ci gaba da kwashe danyen man.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, wanda kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, ya tattauna da kamfanin NNPC, kan ci gaba da aikin haƙo man na Kolmani.