Kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (ko JKS) karo na 20, ya zartar da kudurin kara zurfafa gyare-gyare don inganta zamanantar da kasar, a yayin cikakken zaman taronsa na 3 da aka kammala jiya Alhamis a birning Beijing.
Yayin taron manema labarai da aka kira yau Juma’a game da taron, mataimakin shugaban ofishin kula da nazarin manufofi na kwamitin kolin Tang Fangyu, ya ce zartas da kudurin shi ne sakamako mafi muhimmanci da aka cimma a taron.
- Kwamitin Kolin JKS Ya Amince Da Kudurin Kara Zurfafa Sauye-sauye Daga Dukkanin Fannoni
- Zanga-zangar Tsadar Rayuwa: Ina Mafita?
A cewarsa, kudurin wanda ya kunshi bangarori 15, ya gabatar da matakan gyare-gyare sama da 300.
A nasa bangare, Han Wenxiu, mataimakin daraktan ofishin kula da harkokin kudi da na tattalin arziki na kwamitin kolin JKS, ya ce tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da kasancewa mai karko da aminci yayin da ake fuskantar wasu kalubale, yana mai cewa, kasar za ta kara kyautata aiwatar manufofin kudi daga manyan fannoni. (Fa’iza Mustapha)