Kwamitin Majalisar Wakilai na wucin- gadi kan binciken dalilin tsaikon da aka samu wajen kammala tagwayen hanyar mota kilomita 375 daga Abuja- Kaduna- Kano ya fara gudanar da aikinsa tare da alwashin ganin an kammala aikin cikin lokaci.
Shugaban kwamitin na wucin-gadi, Hon. Abdussamad Dasuki ya bayyana cewar ko kadan ba su da manufar bita- da- kulli ga kowa a binciken illa domin shawo kan kalubalen da ke akwai na tsaikon kammala hanyar wadda Gwamnatin Tarayya ta sake bayar da kwangilar shimfidawa a 2020.
- Gwamnatin Kaduna Za Ta Yi Bincike Kan Ruftawar Masallacin Fadar Zazzau
- Majalisar Dokokin Kaduna Ta Amince Da Kwamishinoni 13
Hon. Dasuki wanda ya jagoranci manbobin kwamitin a ziyarar gani da ido a babbar muhimmiyar hanyar, ya kuma bayyana cewar binciken na da manufar ganin an aiwatar da dukkanin sharuda da ka’idojin da aka shata a kwangilar.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewar a yayin rangadin, kwamitin karara ya nuna rashin gamsuwa kan yadda akin ke tafiya da nuna damuwa kan yiyuwar kammala aikin a sabon wa’adin 2025 da Ma’aikatar Ayyuka ta ayyana.
Tun da farko, kwamitin ya gayyaci kamfanin Julius Berger da ke aiwatar da kwangilar da jami’an Ma’aikatar Ayyuka domin jin ta bakin su kan dalilin da yasa duk da makuddan kudaden da aka fitar kan aikin, amma aikin yana nesa ga wa’adin kammalawa. Jami’in kamfanin ya bayyana cewar aikin ya samu tsaiko ne a dalilin rashin tsaro da ke akwai a hanyar.
A zaman tattaunawa da jami’an Ma’aikatar Ayyuka da kwamitin ya gudanar a karkashin jagorancin Hon. Dasuki, Babbar Sakataren Ma’aikatar, Mamuda Mamman ya bayyanawa kwamitin cewar an kusa kammala aikin sashe na 2 da na 3 na hanyar.
Ya bayyana cewar aikin hanyar a sashen Abuja- Kaduna ya fuskanci matsalar aiwatarwa ta kudi da matsalolin tsaro. Ya ce kusan kashi 20% ne a ka kammala a sashe na 1 daga Abuja zuwa Kaduna, amma ya baiwa kwamitin tabbacin kammala aikin a Mayu 2025.
A yanzu haka dai Kwamitin dai na wucin-gadi yana ci-gaba da aiwatar da aikinsa tare da tsammanin kai rahoto ga Majalisar Wakilai a cikin wa’adin makwanni hudu da majalisa ta baiwa kwamitin.