ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Duniya Ba Ta Bukatar Wani Sabon “Yakin Mummuke”

by CMG Hausa
3 years ago
Yakin Mummuke

Tun lokacin da gwamnatin Joe Biden ya fitar da rahoton dabarun tsaro na kasa a watan Oktoba 2022, Amurka ta shirya tsauraran matakai don mummuke kasar Sin. Gabar da take yi da kasar Sin na dada ta’azzara, ciki har da rikicin fasaha na baya-bayan nan wanda ake kira “Chip war”. Wannan matakin da Amurka ta dauka na nuni da sabon “Yakin cacar baki”. Wanda fadar Washington ta kaddamar ba tare da shawarar kowa ba. Kuma wannan mataki ya sabawa yadda zamani ke tafiya a yanzu. 

Al’umman Amurka na fama da mabanbanta matsaloli a cikin ’yan shekarun nan, musamman tabarbarewar tsarin siyasarta, tsadar rayuwa, korafe-korafe daga al’umma da rashin jituwa tsakanin jam’iyyun siyasar kasar, wadanda su ne ainihin tushen matsaloli da ya kamata ta magance. A maimakon haka, suke ƙoƙarin canza matsin lambar cikin gida da kasar ke fuskanta ta hanyar zuzuta abin da suke kira “barazana daga waje” wato kasar Sin.

ADVERTISEMENT
  • Hanyar Mota Daga Gabashi Zuwa Yammacin Aljeriya Kyakkyawan Misali Ne Ga Hadin-Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Raya Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”

A zahiri kuma, ’yan kasuwan Amurka sun nuna rashin amincewarsu a aikace yadda Amurka ke tafiyar da lamarin. Misali, tun farkon wannan shekara, sashe daga cikin shugabannin shahararrun kamfanoni suke dafifi zuwa kasar Sin don bincika damar hadin gwiwa. Bari mu fara da Starbucks, Sabon Shugaban kamfanin na kasa da kasa Laxman Narasimhan ya shaida girman damar dake akwai a kasuwar Sin. Shugaban Tesla Elon Musk ya bayyana a fili rashin amincewarsa da wannan lakabin da kasashen yamma suka yi wa Sin na “hadari” tare da yanke mu’amala da ita. Shugaban Nvidia Jensen ya ce ba su shirya “raba gari da Sin” saboda ba su da ikon yin haka, kuma kasancewar kasar Sin daya ce tak a duniya. Duk wadannan na nuni da irin muhimmancin kasuwar Sin game da kamanta adalci da tabbatar da moriyar juna.

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Manyan Tarurruka 3 Game Da Kimiyya Da Fasaha A Beijing

Rahoton Bankin Duniya: Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Dore

Amma ga mutanen Amurkawa, ko da yake yankin Sin da Amurka suna da tazara da juna, akwai dadadden musayar zumunta tsakanin kasashen biyu mai dogon tarihi. Labaru da dama sun kara jadadda wannan matsayi: labarin damisa masu tashi wato “flying Tigers” a lokacin Yaƙin Duniya na II, labarin “Guling Friends” a lardin Fujian dake gabashin Sin da kuma abota tsakanin Sin da Amurka ta “house in Muscatine” a jihar Iowa, da dai sauransu.

Tun lokacin barkewar rikicin Ukraine, kasashen Turai suka bi bayan ƙaddamar da takunkumai mabanbanta a kan Rasha, wanda ya koma kansu ya kuma karfafa rikicin makamashi da hauhawar farashin kayayyakin kasashensu. Tun daga wannan lokaci ne kasashen yamma suka fara nazari kan dangantakarsu da kasar Sin. Kwanan baya, shugaban kasar Faransa Emmanuel Mackron ya bayyana adawarsa game da shishigin Nato a yankin Asiya-Pacific. Kasashe Membobin Tarayyar Turai kamar Jamus, Hungary da Serbia sun bayyana a fili cewa ba za su “daina mu’amala” da Sin ba.

Muhimmin dalilin takun-saka tsakanin Amurka da Sin yana ta’allaka ne da irin tsarin manufofin Amurka a kan sauran kasashen duniya, wanda yake haifar da rashin jituwa tsakanin kasashen guda biyu. Ita kasar Sin ta fahimci alfanun dake cikin samun nasara tare, a yayin da ita kuma Amurka ta gwammace ta yi babakere.

“Duniya tana da girman da za ta dauki ci gaban kowace kasa ba tare da wani ya nuna fifiko ba.” Yayin zantawarsa da sakatare Tony Blinken na gwamnatin Amurka a kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinpingy a ce, Sin da Amurka na iya yin hadin gwiwa don samun nasarorin da za su amfanar da daukacin duniya. Hadin gwiwa tsakanin ƙasashen guda biyu masu mafi girman tattalin arzikin duniya zai daidaita zaman lafiyar duniya, tare da ba da gudunmawa ga raya lamurra da manufofin kasashe masu tasowa.

Akwai dalilai da dama da za su sanya manyan giwaye biyu su yi zaman jituwa a cikin daji don bunkasuwa jejin da sauran dabbobin dake cikin shi. Ya kamata Amurka ta daina kumfar baki a kan abubuwan da ba su shafe ta ba. Misalin wannan shi ne sakon da ta aike tarayyar Najeriya a makon da ya gabata inda ta bukaci shugabannin Najeriya su yi taka tsantsan da basussukan da take ciyowa daga kasar Sin. Ya kamata Amurka ta maida hankali a kan daidaita matsalolinta na cikin gida saboda a halin yanzu “Duniya ba ta bukatar wani yakin mummuke”.

Yakin Mummuke
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

An Gudanar Da Manyan Tarurruka 3 Game Da Kimiyya Da Fasaha A Beijing
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Manyan Tarurruka 3 Game Da Kimiyya Da Fasaha A Beijing

July 8, 2026
Rahoton Bankin Duniya: Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Dore
Daga Birnin Sin

Rahoton Bankin Duniya: Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Dore

July 7, 2026
Binciken CGTN Ya Shaida Kiraye-kirayen Jama’a Game Da Bukatar Hada Karfi Da Karfe Wajen Shawo Kan Kalubalen Tsanantar Yanayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Shaida Kiraye-kirayen Jama’a Game Da Bukatar Hada Karfi Da Karfe Wajen Shawo Kan Kalubalen Tsanantar Yanayi

July 7, 2026
Next Post
Sin Da Angola Sun Yi Taro Kan Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya

Sin Da Angola Sun Yi Taro Kan Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Waɗanda Aka Sace A Taraba

Sojoji Da NDLEA Sun Kama Mutanen Da Ake Zargi Da Kai wa ’Yan Ta’adda Miyagun Ƙwayoyi A Katsina

July 8, 2026
An Gudanar Da Manyan Tarurruka 3 Game Da Kimiyya Da Fasaha A Beijing

An Gudanar Da Manyan Tarurruka 3 Game Da Kimiyya Da Fasaha A Beijing

July 8, 2026
Majalisar Zartarwa Ta Jihar Kaduna Ta Amince Da Manufofin Haɓaka Walwalar Al’ummar Jihar

Majalisar Zartarwa Ta Jihar Kaduna Ta Amince Da Manufofin Haɓaka Walwalar Al’ummar Jihar

July 8, 2026
Dole Ne Mace Ta Gaya Wa Mijinta Gaskiya Domin Ranar Hisabi – Matar Gwamnan Jigawa

Gwamnatin Jigawa Ta Ɗaga Mafi Ƙarancin Fansho Zuwa Naira 20,000

July 8, 2026
Rahoton Bankin Duniya: Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Dore

Rahoton Bankin Duniya: Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Dore

July 7, 2026
Binciken CGTN Ya Shaida Kiraye-kirayen Jama’a Game Da Bukatar Hada Karfi Da Karfe Wajen Shawo Kan Kalubalen Tsanantar Yanayi

Binciken CGTN Ya Shaida Kiraye-kirayen Jama’a Game Da Bukatar Hada Karfi Da Karfe Wajen Shawo Kan Kalubalen Tsanantar Yanayi

July 7, 2026
Gwamnatin Tarayya Na Biyan Tallafin Man Fetur A Asirce – El-Rufai

Ɗan Takarar Gwamnan Kaduna Na ADC, Ya Gana da El-Rufai, Ya Sha Alwashin Kawo Karshen Mulkin APC

July 7, 2026
Kulla Yarjejeniyar UNCLOS Da Aiwatar Da Ita Jigo Ne Na Wanzar Da Gaskiya Da Adalci A Odar Teku Tsakanin Kasa Da Kasa

Kulla Yarjejeniyar UNCLOS Da Aiwatar Da Ita Jigo Ne Na Wanzar Da Gaskiya Da Adalci A Odar Teku Tsakanin Kasa Da Kasa

July 7, 2026
Argentina Ta Kai Zagayen Kwata Fainal Bayan Nunawa Egypt Ƙwanji

Argentina Ta Kai Zagayen Kwata Fainal Bayan Nunawa Egypt Ƙwanji

July 7, 2026
Gwajin Harba Makamai Masu Linzami Aiki Ne Na Horarwa Da Sojojin Kasar Sin Ke Gudanarwa

Gwajin Harba Makamai Masu Linzami Aiki Ne Na Horarwa Da Sojojin Kasar Sin Ke Gudanarwa

July 7, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.