Wannan lokaci ne na murna ga dalibai, iyaye, da al’ummar yankin raya karkara ta gundumar Vulpi a Karamar Hukumar Numan a Jihar Adamawa, yayin da dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Demsa/Numan/Lamurde ya gina musu dakin zana jarabawa.
Da yake gabatar da jawabi a taron, shugaban makarantar GDSS Gamadio, Mista Zacheaus, wanda ya nuna farin cikinsa, ya bayyana yadda daliban ke tafiya kananan hukumomin Lamurde da Demsa makwabciyarsu domin rubuta jarrabawar WAEC da NECO.
- Shekarau Ga Tinubu: Ka Rage Yawan Ministocinka Domin Rage Kashe Kudade
- An Gano Dukiyar Iyalan Masarautar Saudiyya Ta Fi Ta Masu Arzikin Duniya Biyu Yawa
Ya bayyana cewa ko da aka kafa cibiyoyin WAEC da NECO a shekarar 2019, dole ne a dakatar da darusa don barin ajujuwan da za a yi amfani da su har tsawon lokacin zana jarrabawar, saboda matsalar rashin dakin zana jarabawar da za a yi wa dalibai.
Shugaban ya kuma yi kira ga dan majalisar da ya kara kaimi, a fannin dakunan gwaje-gwaje na kimiyya da na’ura mai kwakwalwa gami da inganta ajujuwan makarantun domin bai wa dalibai damar karatu mai inganci.
Shi ma da yake jawabi a taron, dan majalisar, Kwamoti La’ori, ya tabbatar wa al’ummar yankin zai ci gaba da jajircewa na ganin sun kai ga morar mulkin dimokuradiyya.
Kwamoti dan majalisa ne da ke kyakkyawar niyya don isar da ayyukan more rayuwa ga al’umma a fadin unguwani 30 na mazabarsa, aikin da masu jawabai da dama a taron suka bayyana da cewa “ba a taba ganin dan majalisa kamar sa ba a tarihin mazabarsa da Jihar Adamawa”.
Dan majalisar bai gushe ba sai da ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da inganta fannin ilimi da kuma kudurin kawo sauyi a rayuwar al’ummarsa.
A yayin jawabinsa, ya nuna jin dadinsa ga jama’a bisa goyon bayan da suke ba shi a kowane lokaci.
Shugabannin kananan hukumomin Numan da Lamurde da sarakunan gargajiya da shugabannin jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki sun gabatar da jawabin fatan alheri, inda suka yaba da salon shugabancin dan majalisar.
Dalibai da daukacin mahalarta taron sun nuna anshuwa da jin dadinsu a cikin jawabai da kasidu da raye-raye da kuma wakokin yabo ga Allah da ya ba su Honorable Kwamoti La’ori, a matsayin wakilinsu.