Mataimakin shugaban ƙasar Iran Javad Zarif, ya yi murabus daga kujerarsa makonni 2 da naɗin da aka masa inda ya ce ya yi hakkan ne saboda kawar da shakku ko kuma yi wa aikin gwamnati zagon kasa.
Sauran dalilan da Zarif ya gabatar sun haɗa da rashin amincewa da jerin sunayen ministocin da sabon shugaban ƙasar Masoud Pezeshkian, ya gabatar wanda a cewarsa ba zai iya aiwatar da manufofin gwamnati ta hanyar da ta kamata ba musamman abinda ya shafi mata da matasa da ƙabilun ƙasar kamar yadda ya yi alkawari.
- Kiran Tada Hankali A Zanga-zanga: Rundunar ‘Yansanda Ta Cafke Wani Dan TikTok A Filato
- Wang Yi Ya Tattauna Ta Wayar Tarho Da Mukadashin Ministan Wajen Iran
A jiya ne dai shugaban ƙasar ya gabatar da sunayen mutane 19 domin tantance su a matsayin ministoci, wanda daga ciki har da mace ɗaya, kuma tuni sunayen suka fara samun caccaka daga masu neman sauyi, ciki harda sunayen da aka saka na tsoffin jami’an gwamnatin Ebrahim Raisi.
Zarif wanda ya jagoranci ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliyar ƙasar a shekarar 2015 da ƙasashen duniya, ya ce sauran matsalolin da yake fuskanta akwai wadda ta shi ‘yayansa da ke riƙe da fasfo ta Amurka, wanda hakan ya saɓawa wata dokar da aka yi a Iran a shekarar 2022 da ta haramta bai wa mutanen da ke rike da fasfo ɗin wata ƙasa muƙamin gwamnati tare da ƴayansu.