ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kwanaki 40: Iyalan Maharban Da Aka Kashe A Edo Na Neman A Biya Su Diyya

by Sadiq
6 months ago
Maharban

Iyalan maharba 16 daga Jihar Kano da aka kashe a garin Uromi, a Ƙaramar Hukumar Esan ta Arewa Maso Gabas a Jihar Edo, sun fito neman a biya su diyya kwanaki 40 bayan kisan ‘ya’yansu.

An kashe maharban ne a watan Maris yayin da suke dawowa gida domin bikin Sallah Ƙarama.

  • Za Mu Magance Matsalar Ruwan Sha Kafin Ƙarshen 2025 A Kaduna – Uba Sani
  • Majalisar Dattawa Ta Kafa Kwamitin Sa Ido Kan Gwamnatin Riƙo A Ribas

Maharban sun fito ne daga ƙananan hukumomin Kibiya, Rano, da Bunkure a Jihar Kano.

ADVERTISEMENT

Iyalan sun taru a harabar sakatariyar Ƙaramar Hukumar Kibiya inda suka yi karatun Alƙur’ani domin roƙar wa mamatan rahamar Ubangiji.

Sun ce har yanzu gwamnati ba ta bayyana matakin da ta ɗauka ba, balle a yi maganar diyya ko hukunta waɗanda suka aikata laifin.

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7

Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso

Malam Bala Dutse, wanda ɗansa Amadu yana cikin waɗanda aka kashe, ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin mantawa da al’amarin.

“An ce an kama wasu, amma har yau ba mu ji komai ba. Na rasa ɗana, kuma rayuwata ta shiga taka mai wuya. Mafi ƙaranci, gwamnati ta fito ta faɗa mana abin da ke faruwa,” in ji shi cikin hawaye.

Hauwa’u Isa, matar ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe, ta ce tana wahala da ’ya’yanta uku.

“Sun ce za su taimaka mana da adalci, amma har yau babu wani taimako. Ba zan daina fatan samun adalci ba, amma har yaushe za mu jira?” in ji ta.

Idan ba a manta ba gwamnonin Kano da Edo, Abba Kabir Yusuf da Monday Okpebholo, sun ziyarci iyalan maharban a baya, inda suka yi alƙawarin za a yi adalci da kuma ba su tallafi.

Gwamna Abba ya kafa kwamitin bincike ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam Gwarzo.

Sai dai bayan kwanaki 40, iyalan na ci gaba da kukan cewa babu wani ci gaba da aka samu.

Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Kibiya, Nasiru Adam Abdulaziz, ya ce ya fahimci halin da ake ciki, amma ya roƙi su da su yi haƙuri.

Ya tabbatar da cewa an kama wasu kuma an kai su Abuja, amma ya nemi a yi shari’a a bainar jama’a domin tabbatar da adalci.

Wannan kisa ya nuna irin matsalar rikice-rikicen ƙabilanci da ake fama da ita a Nijeriya.

Da dama na ganin cewa gwamnati na yin alƙawuran da ba ta cikawa, lamarin da ke hana mutane yarda maganganunta.

Yayin da aka yi addu’ar 40 ta mamatan, iyalansu sun ce ba za su daina nema wa ’yan’uwansu adalci ba.

“Za mu ci gaba da magana har sai an yi mana adalci,” in ji Malam Bala Dutse.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7
Da ɗumi-ɗuminsa

Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7

November 15, 2025
Yanzu Satar Da Kuka Yi Ba Ta Da Amfani: Kwankwaso Ga Gwamnonin APC
Manyan Labarai

Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso

November 15, 2025
NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama
Manyan Labarai

NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama

November 15, 2025
Next Post
Xi Na Kan Hanyar Kai Ziyarar Aiki A Rasha

Xi Na Kan Hanyar Kai Ziyarar Aiki A Rasha

LABARAI MASU NASABA

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan

Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca

Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca

November 15, 2025
Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

November 15, 2025
Za A Yi Gwanjon Rigunan Messi Na Gasar Kofin Duniya Ta 2022 Da Kudi Tsagwagwa

Ina Son Kasancewa Cikin Koshin Lafiya Kafin Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Messi

November 15, 2025
Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci

Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci

November 15, 2025
Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA

Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA

November 15, 2025
Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo

Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo

November 15, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7

Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7

November 15, 2025
An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka

An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka

November 15, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Taka-tsantsan Da Batun Yankin Taiwan 

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Taka-tsantsan Da Batun Yankin Taiwan 

November 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.