A yau Talata ne aka sanar da cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya dare wani sabon mataki a shekarar 2022 duk da tarin kalubalen da aka fuskanta. Haka kuma, kungiyar ingiza cinikayya ta kasar Sin, ta gabatar da rahoto kan muhallin kasuwanci mai jarin waje na kasar a cikin rubu’i na 4 na bara, wanda ya nuna cewa, yawancin kamfanonin dake da jarin kasashen waje, sun gamsu da muhallin kasuwanci na kasar Sin.
Da farko dai, wannan rahoto ne na rubu’i na 4 na shekarar 2022 da muka yi bankwana da ita, lamarin dake nuna cewa, duk da yanayin da tattalin arzikin duniya ke ciki, da sukar da Sin ta sha daga yammacin duniya saboda matakanta na yaki da COVID-19, masu zuba jari na da kwarin gwiwa kan karfin tubalin tattalin arzikin kasar mai juriya da kuma muhallin kasuwanci na kasar, wanda akai-akai gwamnati ke nacewa wajen kyautata shi tare da gyara jerin bangarorin da baki za su iya zuba jari domin ba su dama kamar takwarorinsu na kasar. Haka kuma, ya tabbatar da cewa, masu zargin Sin ta kawo tsaiko ga tattalin arzikin duniya, bata sunan kasar kawai suke, domin cimma wasu muradunsu.
Na biyu, yadda Sin take kara fadada bude kofarta, wani babban kuzari ne ga masu zuba jari. Yayin da wasu manyan kasashen duniya ke ayyana matakan kariyar cinikayya, Sin mai babbar kasuwa ta ci gaba da bude kofarta da maraba da masu zuba jari daga waje, domin ganin an gudu tare da tsira tare, wato an samu wadata a duniya baki daya.
Na uku, ba za a taba raba kyautatuwar jarin waje da bunkasar tattalin arzikin kasar, da kwanciyar hankali da ci gaban da take morewa ba. Babu wanda zai zuba jari a inda ba zai samu riba ko kuma inda dukiyarsa za ta salwanta. Kowa na son zuba jari ne a wajen dake da kwanciyar hankali da tsaro da karfin doka, don haka, yadda kasar Sin ta dage wajen tabbatar da tsaron al’ummarta da muradunta, sun taka rawa gaya wajen jan hankalin masu zuba jarin da ma bunkasar jarin nasu. Haka kuma, ci gaban da take samu ta fannin walwalar al’umma da wadata, shi ma wani abu ne dake jan hankalin masu zuba jarin. Wannan ya kara tabbatar da cewa, al’ummar Sinawa sun yi adabo da talauci, inda suke cikin matsakaiciyar wadata.
Yayin da aka shiga sabuwar shekara aka kuma fara aiwatar da sabbin matakan kasuwanci da na kandagarkin COVID-19 a kasar Sin, ba shakka wata sabuwar dama ce ta samu ga masu zuba jari. Na yi imanin a bana, za a samu habakar jarin waje fiye da wanda aka samu a shekarun baya, lamarin da zai taka rawa wajen habakar tattalin arzikin kasar da ma na duniya. (Fa’iza Mustapha)