Ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar NNPP, Alhaji Aminu Ringim, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, shi ne kaɗai ɗan siyasar da ya cancanta ya maye gurbin marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
A wata hira da manema labarai a Abuja, Ringim ya ce irin ayyukan ci gaban ɗan Adam da na gine-gine da Kwankwaso ya yi a lokacin gwamnatinsa a Kano ne suka tabbatar da cancantarsa. Ya kwatanta Kwankwaso da fitattun shugabannin arewa kamar Sir Ahmadu Bello da Malam Aminu Kano, yana mai cewa ya tsaya tsayin daka wajen kare ‘yan ƙasa marasa ƙarfi.
- Kotu Ta Umarci Gwamnatin Bauchi Ta Biya Tsohon Akanta-Janar Naira Miliyan 100
- EFCC Ta Kama Tsohon Babban Jami’in NNPC Kan Zargin Satar Dala Biliyan 7.2
Ringim ya bayyana Kwankwaso a matsayin ɗan siyasa na ƙasa baki ɗaya wanda ke da goyon baya a jihohin da suka haɗa da Katsina, Jigawa, Zamfara, Sokoto, da Kebbi, yana mai cewa irin tasirin da ya ke da shi ya zarce na jihohi ko yankuna. Ya ce: “Kwankwaso ya kafa tafiya mai zurfi fiye da jam’iyya. Ya gina gagarumin gungu na magoya baya, kuma har yanzu yana jan hankalin al’umma daga dukkanin sassa.”
Ya jaddada cewa Kwankwaso ba wai kawai yana magana kan sauyi ba ne, ya kuma aiwatar da shi lokacin da ya kasance gwamna da kuma Ministan Tsaro. Daga cikin manyan ayyukansa akwai ilimi kyauta, da tallafin karatu na waje, da horon sana’o’in dogaro da kai. Ringim ya ce waɗannan su ne irin manufofin da suka ƙunshi falsafar Aminu Kano da kuma hangen nesa irin na Sardauna.
Dangane da yiwuwar komawar Kwankwaso APC, Ringim ya tabbatar da cewa akwai tattaunawa da ake yi ta bayan fage domin jawo shi cikin jam’iyyar. Ya ce: “Kwankwaso wani babban kayan siyasa ne da ba za a iya kyale shi ba. Ko da a APC, akwai masu son dawowarsa saboda yana da manufa mai amfani da al’umma.”
A cewar Ringim, idan ana so a sami cigaban da ya shafi kowa da kowa a Arewacin Nijeriya da ma ƙasa baki ɗaya, to ana buƙatar siyasa irin ta Kwankwaso wadda ke mayar da hankali kan talakawa da gaskiya a mulki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp