Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023 da aka gudanar a Jihar Kano a ranar Asabar.
Kwankwaso ya doke babban abokin hamayyarsa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 517,341.
- Atiku Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa A Jihar Kebbi
- Yawan Kudin Shiga Da Duk Wanda Ya Fito Daga Kangin Talauci A Xinjiang Ya Samu A Bara Ya Kai RMB Yuan 14,951
Ya ce dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, wanda ya zo na uku da kuri’u 131,716, yayin da dan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi ya samu kuri’u 28,513.
Da yake jawabi jim kadan bayan kammala tattara sakamakon zabe a hedikwatar INEC a Kano, jami’in zaben na jihar, kuma mataimakin shugaban Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Lawan Sulyman Bilbis, ya ce Jihar Kano mai rijistar zabe kimanin 5,792,848, ta samu adadin masu kada kuri’a 1,769,525 a lokacin zabe.