• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kwararre Dan Kasar Croatia : “Double 11” Ya Nuna Juriyar Tattalin Arzikin Kasar Sin

by CGTN Hausa
2 years ago
Double 11

Yawan kunshin kayayyaki da aka tattara a lokacin “Double 11”, bikin cin kasuwar kasar Sin mai kama da Black Friday, ya tabbatar da juriya da farfadowar tattalin arzikin kasar Sin daga annobar COVID-19, kamar yadda Kresimir Macan, wani kwararre a fannnin tattalin arziki dan kasar Croatia, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a wata hirar da aka yi da shi a ranar Litinin. 

“Mutane da yawa sun yi ikirarin cewa tattalin arzikin kasar Sin na fuskantar munanan yanayi, kuma yawan kayayyakin da take samarwa ya ragu, yayin da aka samu akasin hasashen da aka yi. Sai dai sabbin bayanai sun karyata hakan, kuma sun nuna juriya da farfadowar tattalin arzikin kasar”, a cewar Macan.

  • Yadda Ma’aikatan MDD A Nijeriya Suka Girmama Takwarorinsa Da Aka Kashe A Gaza
  • Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Shekara-shekara Na ’Yan Kasuwan Mashigin Taiwan

Hukumar kula da sakonni ta kasar Sin ta ce, daga ranar 1 zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba, kamfanonin aika sakonni a duk fadin kasar sun tattara kimanin kunshin kayayyaki biliyan 5.26, wanda ya karu da kashi 23.22 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara. A ranar 11 ga Nuwamba kadai, an tattara jimillar kunshin kayayyaki miliyan 639, wanda ya ninka da kashi 1.87 na adadin kasuwancin yau da kullun, wanda ke wakiltar karuwar kashi 15.76 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.

An yi hasashen GDP na kasar Sin zai karu da kaso 5.4 cikin dari a shekarar 2023, a cewar sanarwar da asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fitar a ranar 7 ga watan Nuwamba. Macan ya yi nuni da cewa, sauran cibyoyin hada-hadar kudi kamar JP Morgan, da USB da Bankin Deutsche, sun daga matsayin hasashen ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a bana.

“Duk wadannan suna nuni ne da karkon tattalin arzikin kasar Sin,” a cewar Macan, ya kuma kara da cewa farfadowar na da kyau ga kasar Sin da ma duniya baki daya. (Muhammed Yahaya)

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

November 1, 2025
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Daga Birnin Sin

Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

November 1, 2025
Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

November 1, 2025
Next Post
Kasar Sin

Kasar Sin Ta Bukaci Kasa Da Kasa Su Mara Baya Wajen Kawar Da Makaman Nukiliya Daga Gabas Ta Tsakiya 

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

November 1, 2025
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

November 1, 2025
Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

November 1, 2025
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 1, 2025
Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

November 1, 2025
Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

November 1, 2025
Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?

Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?

November 1, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci

November 1, 2025
Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

November 1, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.