Kwararru da masana da jami’an diflomasiyya sama da 100 daga Sin da kasashen Afirka, sun gudanar da wani taron musayar ra’ayoyi dangane da wayewar kan Sin da Afirka, inda suka tattauna alakar hakan da tarin kalubalen dake addabar duniya a halin yanzu.
Taron ya gudana ne a ranar Laraba, a birnin Ismailia na arewa maso gabashin kasar Masar, bisa taken “Dabi’un zamani daga hikimar da aka gada—nazari da hangen nesa daga wayewar kan Sin da Afirka dangane da tarin kalubalen dake addabar duniyar yau.”
- Gwamnati Ta Ware Wata 14 Don Kammala Aikin Hanyar Abuja Zuwa Zariya
- Jami’ai: Kasar Sin Ta Ci Gaba Da Zama Babbar Abokiyar Ciniki Da Ba Da Gudummawa Ga Ci Gaban Afirka
A jawabinsa na bude taron, shugaban cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewa ta kasar Sin ko CASS a takaice Gao Xiang, ya ce taron baya ga amfaninsa a fannin aiwatar da sakamakon taron FOCAC na 2024 da ya gabata a birnin Beijing, a daya hannun ya shaida yadda ake zurfafa manufofin wayewar kan daukacin al’ummun duniya, da sadaukar da basira wajen gina manufar samar da al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya a sabon zamani.
Gao ya kara da cewa, Sin da kasashen Afirka sun zamo misali na bunkasa hadin gwiwar kasashe masu tasowa, suna kuma gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama, kana sun nunawa duniya cewa kasashe masu tasowa na da ikon samar da sabon salon wayewar kan bil’adama na kashin kan su, kuma za su iya bin tafarkin zamanantarwa da ya sabawa na yammacin duniya.
A nasa bangare kuwa, daraktan hukumar lura da harkokin waje na kasar Masar Ezzat Saad, cewa ya yi shawarar da Sin ta gabatar ta aiwatar da manufofin zamanantar da duniya, ta samar da karin sassan hadin gwiwarta da kasashen Afirka, tare da yayata kusancin sassan biyu ta fuskar amincewa da juna da hadin gwiwarsu.
Saad ya ce, ta hanyar dandaloli irin na wannan taron, sassan biyu sun samu zarafin karfafa alakar al’adu, da ingiza kafuwar kawance na tsawon lokaci bisa tushen cimma moriyar bai daya da kara fahimtar juna. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp