Hukumar kwastam ta Nijeriya (NCS), ta bayyana dimbin nasarorin da ta cimma a kasa da makonni biyo da kafa rundunar ‘Operation Whirld Wind’ a Adamawa da Nijeriya baki daya.
Shugaban hukumar, Bashir Adewuli Adeniye, ya shaida wa manema labarai haka a ranar Litinin a Yola. Ya ce an samu karuwar safarar man fetur da hukumar NCS tare da hadin gwiwar ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro (NSA), inda aka kaddamar da ‘Operation Whirld Wind’ domin gudanar da ayyuka a fadin kasar nan.
- Tinubu Ya Ba Jama’an Tsaro Umarnin Kamo Ƴan Ta’addan Da Suka Kashe Mutane A Katsina
- ‘Yansanda Sun Hana Hawan Sallah A Kano
Ya ci gaba da cewa, “Nijeriya na cin gajiyar kayyade farashin man fetur daidai da hangen nesa na Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kare kudin kasa da rage matsi da kila ake dangantawa da ayyukan fasa-kwaurin man fetur,” in ji Adewuli.
Shugaban hukumar kwastam ya kuma sanar da gagarumin ci gaba da aka samu ta hanyar kafa rundunar a cikin makonni 2 da suka gabata, “Mun samu sahihin ba-yanan sirri kan daidaiton farashin man fetur a kusa da jihohin da ke kan iyaka, wanda hakan ke nuni ga masu fasa kwaurin ba za su cimma nasara ba.
“A cikin kwanaki 7, an kama litar mai da ya kai 150,950, wanda kudinsa ya kai nai-ra 105, 965, 391 a wurare daban-daban a fadin Nijeriya, a ranar 31 ga Mayu, 2024, mun kama wata tanka da lita 45, 000 na PMS a Moba na Jihar Adamawa.
“A ranar 1 ga watan Yuni 2024, mun kama wata tankar da lita 45, 000 na PMS a Mubi, ranar 3 ga Yuni 2024 mun kama lita 2,375 na PMS a cikin Jerrycan lita 95 a Mubi, ranar 5 ga watan Yunin 2024 mun kama lita 4,450 na PMS a cikin jerrycan lita 178, a wurare guda uku da suka hada da Song, Wuroboki, Mubi Gidan Mada-ra-Sahuda.
“A ranar 6 ga watan Yunin 2024, mun kama lita 20,30 na PMS a cikin lita 25 da 30 na Jerrycan a wurare daban-daban a fadin Nijeriya, ciki har da Maiha da ke Ada-mawa, Illela, Jihar Sakkwato da Agbaragba Rafi da ke kan iyakar Mfum na Jihar Kuros Ribas, ” in ji shi.