ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Itatuwan Banyan Biyu Suna Shaida Yadda Ake Gadon Tunani Tsakanin Xi Jinping Da Mahaifinsa

by CGTN Hausa
2 years ago
Xi Jinping

A ranar 12 ga watan Maris na shekarar 2000, Xi Zhongxun mai shekaru 87 da iyalinsa suka dasa itacen Banyan tare, a gidansu da ke birnin Shenzhen. A matsayinsa na daya daga cikin manyan jagorori da kuma muhimman wadanda suka soma gudanar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje a lardin Guangdong, Xi Zhongxun ya dasa wannan itacen Banyan don bayyana fatansa na samun wurin zama a wannan yanki don yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga waje.

A cikin shekaru fiye da biyu da ya dauka yana aiki a Guangdong, Xi Zhongxun ya jagoranci gudanar da ayyuka da yawa. Jerin sabbin matakan da ya dauka, sun aza harsashi ga lardin na jagorantar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin baki daya.

  • Sadaukar Da Kai Ga Hidimtawa Jama’a: Tasirin Mahaifin Xi Jinping A Kan Dansa
  • Xi Jinping Ya Taya Cyril Ramaphosa Murnar Sake Zama Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu

A farkon manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, muhimmin aikin mahaifinsa na jagorantar al’ummar Guangdong wajen ‘yantar da tunaninsu da ci gaba da yin gyare-gyare ya yi tasiri sosai ga Xi Jinping.

ADVERTISEMENT

Wani masanin Amurka ya bayyana cewa, aikin da kasar Sin ta yi na yaki da cin hanci da rashawa, gyare-gyare ne. Gudanar da mulki bisa doka, gyare-gyare ne. Kawar da fatara, shi ma yana cikin gyare-gyare, sake fasalin aikin soji, da sake fasalin jam’iyya da hukumomin gwamnati, dukkansu gyare-gyare ne. Wani masanin da ya gudanar da aikin rubuta daftari kan cikakken zama na uku na kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, ya tunatar da cewa, “da ba don aniyar Xi Jinping ba, da zai yi wuya a iya fito da wasu manyan gyare-gyare masu yawa.”

A shekarar 2012, bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, Xi Jinping ya zabi lardin Guangdong a matsayin zango na farko da ya yi rangadin aiki a kananan hukumomi. A wurin shakatawa na Lianhuashan da ke birnin Shenzhen na lardin, ya ajiye kwandon furanni ga gunkin tagulla na Deng Xiaoping, tare da dasa itacen Banyan a filin Shanding.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Yanzu, itatuwan Banyan guda biyu da Xi Zhongxun da Xi Jinping suka dasa daya bayan daya a Shenzhen, sun riga sun girma sosai. Kasar Sin da ta mayar da lardin Guangdong a matsayin mafarin yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, bayan samun gagaruman sauye-sauye a kasar, yanzu tana kokarin tsara wani sabon tsari na raya kasa mai mulkin gurguzu ta zamani a dukkan fannoni, tare da kokarin cimma babban buri na gina kasa mai karfi da farfado da al’umma. (Bilkisu Xin)

Xi Jinping
CGTN Hausa
+ postsBio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Matsalolin Ilimi A Nijeriya Da Hanyoyin Gyara Su (1)

Matsalolin Ilimi A Nijeriya Da Hanyoyin Gyara Su (1)

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.