Hukumar Hana Fasa-Kwauri ta Kasa (Kwastam) a Jihar Kebbi ta samu nasarar kama wasu kayan sawa na hannu na kimanin Naira miliyan 36 da kuma samar da Naira miliyan 127 a matsayin kudin shiga a watan Nuwamba.
Shugaban Hukumar Kwastam, Kwanturola Joseph Attah ne, ya bayyana hakan ga manema labarai a Birnin Kebbi, yayin da yake baje kolin kayayyakin da hukumar ta kama a watan da ya gabata.
- Kyawawan Halaye 2: Wasu Annabawa Da Sauran Bayin Allah Da Suka Yi Magana A Tsummar Jego
- Shugaban Kasar Sin Ya Yi Shawarwari Da Manyan Shugabannin Kasar Saudiyya Da Kuma Gana Da Shugabannin Wasu Kasashen Larabawa Bi da Bi
Da yake ba da cikakken bayani kan ayyukan rundunar, Attah ya ce, rundunar ta samu kudi miliyan dari da ashirin da bakwai, da dubu dari takwas da talatin da tara, da naira dari uku da casa’in (127,839,390.75) a matsayin kudaden shiga daga shigo da kayan fasa-kwauri a kan hanyar iyakar Kamba da ke Jamhuriyar Nijar daga Jihar kebbi.
A bangaren yaki da fasa-kwauri, ya bayyana cewa, a yayin da ake ci gaba da sintiri a fadin Jihar Kebbi, rundunar ta samu nasarar kame wasu kayayyaki da suka hada da dila 303 da buhu 94 na tufafin gwanjo guda 94, mota kirar BMW guda daya, lita mai 2,375 a cikin jarkoki da kuma buhunan shinkafa 58 na kasar waje mai nauyin kilo 50 kowanne; da sauran wadanda kudin harajinsu ya kai miliyan arba’in da shida, da dubu dari bakwai da shida, da naira dari bakwai da casa’in da biyar (46,706,795.00).
Haka kuma, Kwanturola Joseph Attah, ya ba da tabbacin cewa jami’ansa a shirye suke su dakile ayyukan masu fasa-kwauri saboda rundunar tana da kayan aikin da suka dace don gudanar da aikin a kowane lokaci.
“Daga bayanan da muka samu, an samu karuwar kayan fasa-kwauri a cikin watanni biyu da suka gabata.”
“Idan za a tuna cewa an kuma kama dilar gwanjo 139 a watan Oktoba.
“Masu fasa-kwaurin suna biyan bukatun mutane masu kauri irin su cardigans a wannan lokacin na sanyi don safarar wadannan tufafin da aka yi amfani da su, ba tare da la’akari da tasirin kiwon lafiya ba har zuwa karshen amfani da su.
“Ba mu san daga ina kayan suka fito ba ko kuma na karshe masu amfani da tufafin, yanayin lafiyarsu da sauransu.
“Don guje wa shakku, tufafin hannu na biyu sun fado a karkashin jadawalin kasuwanci na (CET) 2022-2026, wanda aka haramta shigo da shi a kasan lafiya. Batun fasa kwaurinta ya ci karo da sashe na 46 na dokar hukumar kwastam (CEMA) CAP C. 45 LFN, 2004 (kamar wadda aka yi wa kwaskwarima).
“Hakkin hukumar kwastam ne ta tabbatar da cewa ba a bar wani abu da zai iya cutar da mutanen kasa ba. Mun kuduri aniyar yin hakan,” in ji shi.
Hukumar ta yaba da tallafin da hukumar ke bayarwa ta hanyar samar da dabaru kuma ta kuduri aniyar tunkarar masu fasa-kwauri a jahohin kasar nan.
Hukumar ta CAC ta yi kira ga duk masu hannu da shuni da su tallafa wa rundunar ofishin Kwastam na Jihar Kebbi ta hanyar samar da bayanai masu inganci don samun nasarorin gudanar da ayyukan dakile fasa-kwauri.