Hukumar kwastam reshen jihar Kebbi ta kama wasu kayayyaki na fasa kwabri da harajinsu ya kai Naira Miliyan ashirin da uku, da dubu dari da arba’in da daya, da naira dari takwas da uku (23,141,803) a wurare daban-daban na jihar.
Shugaban yankin, Dakta Ben Oramalugo ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a a hedikwatar ofishin hukumar da ke Birnin Kebbi.
Shugaban Kwastam din, ya ce a cikin watanni biyu da suka wuce ne ya karbi ragamar shugabancin ofishin jihar , inda ya samu gagarumar nasara a fannin samun kudaden shiga, yayin da ya jaddada cewa a cikin watan Maris hukumar ta samu jimillar kudi Naira Miliyan dari da arba’in da hudu, da dubu dari takwas da sittin da biyu, da naira dari uku da saba’in da biyu (N144, 862,372).
“Muna da fatan cimma kudurin hukumar na tara kudaden shiga na shekara- shekara na reshen Kebbi da ya kai Naira biliyan daya da miliyan hamsin da takwas, da dubu dari bakwai da biyu da dari hudu da sittin da shida (N 1, 058,702,466). Sannan za a magance babban kalubalen da masu ruwa da tsakinmu suka gano na biyan haraji da yawa daga kasashen da ke makwabtaka da mu kafin kayayyakinsu su isa iyakar kasa da ke a garin Kamba, wadda ita ce daya tilo da ake budewa a halin yanzu a cikin jihar”, in ji shi.
Ya kara da cewa, kayayyakin da aka kama sun hada da: Fetur lita 16, 375, katan na spaghetti 210 na kasar waje, bale 34 na kayan sawa na hannu da kuma katan 109 na kayan zaki da dai sauransu.
Haka kuma ya kara da cewa “mun samu sahihin bayanan sirri na ayyukan fasakwauri na Fetur a gidan man AP da ke Yauri a karamar hukumar Yauri a jihar, an tura tawagar jami’an hukumar zuwa wurin kuma nan take aka kama su.
“Mun iya kwashe kilogiram dari uku da hudu (304) na Fetur mai lita 25 kowanne, tare da rufe gidan man da ke karamar hukumar da muka ambata tare da tankokin mai gudu shida a cikin gidan man, yanza hakan muna kan bincike kan lamarin.
“Har ilayau masu fasa kwauri da kansu suka dawo tare da wasu ‘yan baranda da nufin hana kwace man na fasa kwauri, amma mutanen mu sun tsaya tsayin daka har zuwa lokacin da muka samu agajin sojojin Nijeriya wadanda suka taimaka mana wajen tarwatsa masu fasa kwaurin.”
Kazalika Shugaban hukumar, Dokta Ben Oramalugo ya gargadi masu fasa kwauri da masu taimaka musu a fadin jihar da su guji aikata munanan ayyukan. Domin a cewarsa, “Ba za mu nade hannu ba, mu bar duk wani gidan man da za a yi amfani da shi a matsayin bututun fitar Fetur daga kasar nan ba, gwamnatinmu na biyan makudan kudade wajen ba da tallafa mai ga ‘yan kasar, wanda hakan ya sa ya zama abin zargi da rashin bin doka ga wasu mutane kalilan su karkatar da man, don bunkasa kansu, inji shi”.
Ya kuma ba da tabbacin hukumar kwastam ta Nijeriya, reshen jihar Kebbi, za ta ci gaba da jajircewa wajen dakile ayyukan fasakwauri ba bisa ka’ida ba, kasancewar suna da kayan aiki. “Bugu da kari muna da horo wajen dakile duk ayyukansu”. Ya bayyana.
Daga nan ya gode wa duk ’yan kasa musamman na jihar da ke taimakawa Kwastam da bayanai masu amfani wajen dakile fasakwaurin da ake yi a jihar.